Jakadun da Tinubu Ya Zaba Sun San Matsayarsu bayan Tantancesu a Majalisa
- Majalisar dattawan Najeriya ta kammala aikin tantance jakadun da Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zaba
- Shugaba Tinubu dai ya gabatar da sunayen mutane 64 ga majalisar domin tantancewa tare da amincewa da su a matsayin jakadu
- A yayin zaman majalisar na ranar Alhamis, an sanar da cewa dukkanin mutanen 64 sun tsallake tantacewar da aka yi musu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta tabbatar da Sanata Jimoh Ibrahim (APC, Ondo ta Kudu), tsohon shugaban hukumar zaɓe ta mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin jakadu.
Hakazalika majalisar ta tabbatar da Sanata Ita Enang, Reno Omokri, Sanata Grace Bent da Sanata Farfesa Nora Ladi Daduut a matsayin jakadu da ba asalin ma'aikatan jakadanci ba.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa majalisar dattawan ta tabbatar da su ne yayin zamanta na ranar Alhamis, 18 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar dattawa ta amince da jakadu
Hakazalika majalisar ta amince da Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohuwar uwargidan gwamnan Imo, Chioma Ohakim, tsohon Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, Femi Fani-Kayode; Erelu Angela Adebayo, Florence Ajimobi.
Jerin ya kunshi jakadu marasa cikakken kwarewa a aikin jakadanci da manyan kwamishinoni 34, da kuma jakadu masu kwarewa a aikin jakadanci da manyan kwamishinoni 30, inda jimillar su mutum 64 baki ɗaya.
Tabbatarwar da aka yi a ranar Alhamis ta biyo bayan gabatarwa da la’akari da rahoton kwamitin harkokin kasashen waje, wanda shugaban kwamitin, Sanata Sani Bello (APC, Neja ta Arewa), ya gabatar, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da hakan.
Daga cikin fitattun sunaye a jerin jakadu 34 masu kwarewa a aikin jakadanci akwai Sulu-Gambari Olatunji Ahmed daga jihar Kwara, Segun Ige daga jihar Edo, da Odumah Yvonne Ehinosen daga jihar Edo.
An gabatar da rahoto kan jakadun kasashe
Da yake gabatar da rahoton, Sanata Bello ya ce an samu dukkan waɗanda aka zaɓa sun cancanci nadin ba tare da wani korafi ko kara a kansu ba.
A tuna cewa yayin aikin tantancewa, an fara kiran Sanata Jimoh Ibrahim, inda aka yi masa tarba ta musamman kasancewarsa Sanata mai ci da zama kuma mamba a kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa.

Source: Facebook
Shugaban majalisa ya taya su murna
A jawabin da ya yi bayan tabbatarwar, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya taya su murna tare da yi musu kira da su wakilci ƙasar nan yadda ya kamata a matsayinsu na jakadun Najeriya a ƙasashen da za su je.
Hakazalika, ya roki Sanata Jimoh Ibrahim da kada ya manta da majalisar dattawa, ya ci gaba da hulɗa da ita domin majalisar ta rika cin gajiyar iliminsa da gogewarsa a kai a kai.
An yi hatsaniya wajen tantance jakadu
A wani labarin kuma, kun ji cewa an dan samu 'yar hatsaniya a zauren majalisar dattawa wajen tantaance jakadu.
An yi 'yar hayaniya bayan a yayin da ake tantance Emmanuel Adeyemi, tsohon ɗan takara daga jihar Ekiti.
Masu aikin tantancewar sun nuna bacin ransu baya Emmanuel Adeyemi ya kasa lissafo sunayen sanatoci uku da suka fito daga jiharsa ta Ekiti.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

