Akpabio: Bayan Yada Jita Jita, An Ji Gaskiyar Batun Rashin Lafiyar Shugaban Majalisar Dattawa

Akpabio: Bayan Yada Jita Jita, An Ji Gaskiyar Batun Rashin Lafiyar Shugaban Majalisar Dattawa

  • An yada jita-jita kan rashin lafiyar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio a cikin 'yan kwanakin nan
  • Hadimin shugaban majalisar, Kenny Okolugbo, ya fito ya yi bayani kan rahotannin da aka yada game da Sanata Godswill Akpabio
  • Mista Kenny Okolugbo ya bayyana cewa akwai bukatar a dauki tsauraran matakai kan masu yada labaran da ba su da tushe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kenny Okolugbo, mai ba shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, shawara kan harkokin sadarwa, ya yi magana kan jita-jitar rashin lafiyar ubangidansa.

Kenny Okolugbo ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta game da rashin lafiyar shugaban majalisar dattawan.

An yada jita-jita kan rashin lafiyar Akpabio
Sanata Godswill Akpabio a zauren majalisa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Hadimin na Akpabio ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata hira da aka yi da shi a shirin 'Morning Brief' na tashar Channels tv a ranar Alhamis, 18 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

NLC: Ajaero ya fadi sabon alkawarin da Tinubu ya dauka game da rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me aka ce kan rashin lafiyar Akpabio?

Kenny Okolugbo ya bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe wadanda babu komai a cikinsu face karya da karairayi.

Ya ce shugaban majalisar dattawan na cikin koshin lafiya kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na hukuma ba tare da wata matsala ba.

“Shugaban majalisar dattawa yana cikin koshin lafiya kwarai. Kun gan shi da idonku, yana halartar zaman majalisa, kuma hakan ya zama amsa kan tambayar ko bai da lafiya."

- Kenny Okolugbo

Ana yada jita-jita kan manya

Kenny Okolugbo ya kawo misalin irin wannan jita-jitar da aka taɓa yaɗawa game da Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, inda aka ce ba shi da lafiya sosai.

Ya ce amma washegari bayan yada jita-jitar aka gan shi yana kaddamar da ayyuka tare da halartar shirye-shiryen kai tsaye.

“Har ma Minista Wike ya fuskanci irin wannan jita-jitar. Wata rana aka ce ya suma ko ya kamu ciwon sashe, amma washegari ya fito yana kaddamar da ayyuka tare da bayyana a shirin kai tsaye."

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta shiga dambarwar Dangote da shugaban NMDPRA

- Kenny Okolugbo

An musanta jita-jitar rashin lafiyar Akpabio
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Akpabio: An bukaci a dauki mataki

Mai taimaka wa shugaban majalisar dattawan ya yi kira da a kara sanya ka’idoji kan amfani da kafafen sada zumunta domin dakile yaɗuwar labaran ƙarya.

“Dole ne a sanya doka kan kafafen sada zumunta. Kowa yanzu yana ɗaukar kansa a matsayin mai wallafa labarai a intanet, amma ba sa fahimtar cewa doka ta haramta yaɗa bayanan da ba ka da tabbaci a kansu."

- Kenny Okolugbo

Majalisa ta mika koke ga ONSA da DSS

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta nuna damuwa kan jita-jitar da aka rika yadawa kan shugabanta, Sanata Godswill Akpabio.

Majalisar ta bukaci Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) da hukumar DSS, su bincika tare da gano mutanen da ke da hannu a rahotannin da ke cewa Akpabio ya rasu a Landan.

Shugaban majalisar ya bukaci ONSA da DSS da su gano tushen labaran karyar da masu yadawa, tare da daukar matakan da suka dace a kansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng