Gwamna Abba Ya Share Hawayen Tsofaffin Kansilolin Kano, Ya Biya Bashin N15.67bn

Gwamna Abba Ya Share Hawayen Tsofaffin Kansilolin Kano, Ya Biya Bashin N15.67bn

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya biya basussukan da tsofaffin kansiloli suka dade suna bin gwamnati kan hakkokinsu
  • Abba Kabir Yusuf ya ware biliyoyin kudi domin biyan hakkokin kansilolin wadanda suka yi aiki a karkashin gwamnatocin da suka gabace shi
  • Sama da kansiloli 3,000 ne suka samu kudin da suka biyo gwamnati bashi a matsayin hakkokinsu wanda aka dade ba a biya su ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kammala biyan dukkanin alawus-alawus da tsofaffin kansiloli suka biyo bashi.

A makon nan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kammala biyan bashin na tsofaffin kansiloli wanda ya taru na tsawon fiye da shekara 10.

Gwamna Abba Kabir ya biya tsofaffin kansiloli hakkokinsu
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen taro Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a ciki wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya fadi biliyoyin da ya tarar a asusun Rivers bayan cire dokar ta baci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Kabir Yusuf ya sallami tsofaffin kansiloli

Gwamna Abba ya ce an raba Naira biliyan 8.26 ga kansiloli 1,371 da suka yi aiki tsakanin shekarun 2021 zuwa 2024.

Biyan kuɗin ya kasance kashi na uku kuma na ƙarshe na shirin warware bashin da gwamnatin ta fara biya tun farkon wannan shekara.

A watan Mayu, an biya Naira biliyan 1.8 ga kansiloli 903 da suka yi aiki daga 2014 zuwa 2017, sannan a watan Agusta aka biya Naira biliyan 5.6 ga kansiloli 1,198 na lokacin 2018 zuwa 2020.

Sanarwar ta bayyana cewa jimillar kuɗin da aka biya a kashi uku ta kai Naira biliyan 15.67, inda sama da tsofaffin kansiloli 3,400 suka amfana.

“Ba wai kawai muna rufe wani shafi na bashi ba ne; muna buɗe sabon babi. Bai kamata a sake barin masu yi wa jama’a hidima cikin rashin tabbas kan haƙƙinsu ba.”

.- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Kara karanta wannan

"Karya kake yi," Tsohon gwamnan Sakkwato ya maida martani mai zafi ga Bello Turji

An fara ba kansilolin yanzu hakkokinsu

Gwamnan ya kuma bayyana cewa kansiloli da ke kan aiki yanzu, waɗanda zangonsu ya fara a 2024, sun karɓi kashi 50 cikin 100 na alawus ɗin kayan ofis, wanda ya kai Naira biliyan 1.27.

Gwamna Abba Kabir ya ba tsofaffin kansiloli N15.67bn
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ya yaba wa ma’aikatar kananan hukumomi, ma’aikatar kuɗi, ofishin babban akanta na jihar, da kungiyar tsofaffin kansiloli bisa tabbatar da sahihanci da gaskiya a aikin tantancewa.

Taron ya samu halartar tsofaffin ’yan majalisa, manyan jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin ƙwadago, inda da dama daga cikinsu suka bayyana biyan kuɗin a matsayin abin da aka daɗe ana jira.

Gwamna Abba ya kafa sabuwar runduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa wata sabuwar rundunar tsaro ta musamman domin tunkarar matsalolin tsaro da suka fara addabar Kano.

Gwamna Abba Kabir ya amince da kafa rundunar ne domin tunkarar matsalolin tsaro a tashoshin mota da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a a fadin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Abba ya dauki sabon mataki don kare rayuka a Kano

Rundunar ta musamman za ta gudanar da tsauraran sintiri, tattara bayanan sirri, da hadin gwiwar ayyukan tsaro a tashoshin mota da sauran wuraren da ke da rauni.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng