An Fara Surutu da Sarki Ya Shirya Nada Dan Shugaban Kasa, Seyi Tinubu a Babbar Sarauta
- An fara surutu da Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade ya sanar da shirinsa na nada Seyi Tinubu a sarautar Okanlomo na Ƙasar Yarbawa
- Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce saboda Ooni na Ife ya nada fitaccen dan kasuwa, Prince Dotun Sanusi a irin wannan sarauta makonni biyu da suka wuce
- Wata takardar gayyata da ta fara yawo a soshiyal midiya ta nuna cewa za a ba 'dan shugaban kasa wannan sarauta ranar Lahadi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - 'Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya samu sarauta daga Mai Martaba Alaafin na jihar Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade.
Rahotanni sun nuna cewa Sarkin zai nada Seyi Tinubu, 'dan gidan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a sarautar Okanlomo na Ƙasar Yarbawa.

Source: Twitter
Seyi Tinubu ya samu sarauta a Oyo
A wata takardar gayyata da ta yadu a kafafen sada zumunta wadda wakilin Leadership ya ci karo da ita, za a gudanar da nadin ɗan shugaban kasar a Oyo ranar Lahadi, 21 ga Disamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan nadi na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya nada sanannen ɗan kasuwa daga Ibadan, Prince Dotun Sanusi, a sarautar Okanlomo Oodua.
Wata majiya daga fadar Alaafin da ke jihar Oyo ta tabbatar da shirin bai wa dan Tinubu sarauta, ta ce za a gudanar da bikin nadin sarautar kamar yadda aka gani a takardar gayyata.
An fara shirye-shiryen nadin Seyi Tinubu
Basaraken, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce kwamitin shirye-shirye da Sarki ya kafa yana aiki ba dare ba rana domin tabbatar da nasarar taron nadin sarautar.
Har ila yau, Moremi Ojudu, Mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa Tinubu kan Huldar Al’umma (Kudu maso Yamma), wacce ke da kusanci da Seyi Tinubu ta tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023
Ta rubuta cikin harshen Yarbanci cewa, "Okanlomo na mu da muke kauna. Ɗan’uwa na musamman. Kudo maso Yamma za ta karbi bakuncin manyan baki."
Rikicin da ya biyo bayan nadin Okanlomo
Idan baku manta ba, mai martaba Alaafin na Oyo ya kalubalanci Ooni na Ife kan nadin Sanusi a matsayin Okanlomo na Ƙasar Yoruba, in ji Tribune Nigeria.
Oba Owoade ya bayar da wa’adin awanni 48 ta bakin mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Bode Durojaye, don a janye wannan sarauta da Oomi ya nada Prince Sanusi.

Source: Twitter
Alaafin ya yi iƙirarin cewa Ooni ba shi da hurumin bayar da duk wata sarauta da ta shafi Ƙasar Yarbawa gaba ɗaya.
An dai fara ce-ce-ku-ce kan nadin da aka shirya yi wa Seyi Tinubu, musamman ganin rikicin da ya biyo bayan nadin Sanusi a matsayin Okanlomo Oodua.
Oluremi Tinubu ta samu sarauta a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta samu sarauta a jihar Gombe da ke Arewacin Najeriya.
Masarautar Akko da ke Jihar Gombe ta nada matar shugaban kasa a sarautar Sarauniyar Yakin Akko, wato Sarauniyar da ke fafutukar kare hakkin marasa galihu.
Lamidon Akko, Alhaji Umar Muhammad Atiku , ne ya ba da sarautar yayin da Uwargidar shugaban ƙasa ke ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Gombe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

