NLC Ta Bukaci Kowane Dan Najeriya Ya Fito Zanga Zanga a Yau Laraba
- Kungiyar kwadago ta NLC ta ce ta gano wasu shirye-shirye da ake yi domin kutsawa cikin zanga-zangar da ta shirya kan matsalar tsaro a Najeriya
- 'Yan kwadago sun bayyana cewa wasu kungiyoyi da mutane da ke aiki a boye na da niyyar haddasa tashin hankali domin bata manufar zanga-zangar
- NLC ta yi gargadin cewa duk wani hari kan masu zanga-zanga na iya haifar da matakai masu tsauri da za su shafi harkokin tattalin arzikin kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar kwadagon Najeriya, NLC, ta ce akwai yunkurin wasu kungiyoyi da mutane marasa kishin kasa na tarwatsa zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a fadin kasar nan.
Zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a yau,17 ga Disamban 2025, na da alaka da kara tabarbarewar matsalar tsaro, ciki har da sace-sace, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe a sassa daban-daban.

Source: Twitter
The Cable ta ce kungiyar ta ce za a yi zanga-zangar ne domin nuna alhini da kuma kira a dauki mataki kan tsaro da jan hankalin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gargadin kungiyar NLC kan hana zanga-zanga
A wata sanarwa da mukaddashin sakataren NLC, Benson Upah, ya fitar, ya ce kungiyar ta samu sahihin bayanan sirri da ke nuna cewa an shirya tura ‘yan daba dauke da makamai domin kai farmaki kan masu zanga-zanga.
Upah ya bayyana cewa manufar wannan yunkuri ita ce haddasa tarzoma da rikici, domin a samu hujjar murkushe zanga-zangar da karfi, abin da zai tauye hakkin jama’a na fadin albarkacin baki.
Ya jaddada cewa NLC ta riga ta fahimci wadannan shirye-shirye, yana mai gargadin duk masu hannu a ciki da su dakatar da ‘yan aikinsu domin kauce wa mummunan sakamako.
Kiran 'yan kwadago ga jami'an tsaro
Kungiyar kwadago ta bukaci rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su dauki nauyin kare rayuka da dukiyoyin masu zanga-zanga.

Kara karanta wannan
Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro
Sanarwar ta ce ‘yan sanda sun riga sun samu bayani kan zanga-zangar da yadda za ta gudana, don haka ya rataya a wuyansu tabbatar da cewa ‘yan kasa sun yi amfani da ‘yancinsu na taruwa da bayyana ra’ayoyi cikin lumana.

Source: Facebook
NLC ta nanata cewa mutunta doka da kundin tsarin mulki wajibi ne, kuma duk wani yunkuri na take wannan hakki zai kara jefa kasar cikin matsala.
NLC ta bukaci kowa ya fito zanga-zanga
Kungiyar ta yi kira ga ma’aikata, marasa aikin yi, dalibai, ‘yan kasuwa da kuma wadanda matsalar tsaro ta shafa kai tsaye da kada su bari tsoro ko barazana su hana su fitowa.
Ta bukaci kowa da kowa da ya halarci zanga-zangar cikin tsari da kuma bin doka domin tabbatar da cewa ta kasance cikin lumana da nagarta.
'Yan kungiyar NLC sun yi barazanar yajin aiki
Kungiyar ta bayyana cewa majalisar zartarwarta ta kasa ta riga ta yanke shawarar daukar mataki mai tsauri idan aka cutar da ko da mutum daya daga cikin masu zanga-zangar.
Vanguard ta rahoto cewa sanarwar ta nuna cewa hakan na iya kai wa ga ayyana yajin aiki na kasa baki daya, matakin da zai shafi tattalin arzikin kasa.
'Zanga-zanga babu fashi' Inji NLC
A wani labarin, mun rahoto muku cewa kungiyar kwadago ta NLC ta jaddada cewa babu fashi a shirin zanga-zangar da ta yi.
Ta bayyana haka ne bayan fara kira ta janye zanga-zangar da za ta yi domin nuna fushi game da rashin tsaro a Najeriya.
Kungiyar za ta yi gangami ne a dukkan jihohi 36 da birnin tarayya Abuja, inda za ta bukaci gwamati ta tashi tsaye a kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

