Gwamna Radda Ya Kafa Tarihi a Bangaren Samar da Wutar Lantarki ga Talakawa

Gwamna Radda Ya Kafa Tarihi a Bangaren Samar da Wutar Lantarki ga Talakawa

  • ƘGwamna Dikko Radda ya kaddamar da tashar samar da wuta daga ruwa, irinta ta farko a yankunan karkara a jihar Katsina
  • Malam Dikko Radda ya aza harsashin gina karamar tashar wutar, wacce ake sa ran za ta wadatar da Danja, Kafur da kewayensu
  • Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Radda ya bayyana aikin a matsayin wani sabon babin ci gaba ga mazauna karkara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da aikin gina tashar wutar lantarki ta ruwa mai ƙarfin megawatt 1 (1MW) a karamar hukumar Danja.

Gwamna Radda ya bayyana aikin mai cike da tarihi a matsayin muhimmin mataki na kawo sauyi ga wutar lantarki a karkara, bunƙasar tattalin arziki da ci gaba mai ɗorewa a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Mangal ya samu mukami da Gwamna Radda ya kaddamar da majalisar sarakunan Katsina

Gwamna Dikko Radda.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda lokacin kaddamar da aikin samar da makamashi a dam din Danja Hoto: Chief Press Secretary
Source: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Mohammed ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook. Ya ce an gudanar da bikin aza harsashin aikin ne a dam ɗin Danja.

Gwamna Dikko Radda ya kafa tarihi

Wannan aiki na gina tashar samar da wutar lantarki daga ruwa a karkara shi ne irinsa na farko da gwamnatin Katsina ta kaddamar a karamar hukumar Danja.

Ana sa ran aikin zai samar da wutar lantarki mai tsafta, araha kuma abin dogaro ga al’ummomin kananan hukumomin Danja, Kafur da kewaye.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Radda ya bayyana aikin a matsayin wani sabon babi ga al’ummomin karkara.

Ya ce:

“Wannan muhimmin aiki alama ce ta makoma mai kyau ga Danja, Kafur da sauran al’ummomin da ke kewaye.
"Muna kokarin amfani da ruwa wajen samar da wutar lantarki mai ɗorewa wadda za ta inganta rayuwa, sana’o’i da bude daamarmakin tattalin arziki kai tsaye,” in ji gwamnan.

Kara karanta wannan

Bayan rantsar da kwamishinoni, Gwamna Umaru Bago ya fatattaki hadimai sama da 25

Radda ya bayyana cewa aikin na nuna jajircewar gwamnatinsa wajen samar da wutar lantarki a karkara, bunƙasa hanyoyin samar da makamashi da kuma tabbatar da tsaronsa.

Alfanun tashar wutar da za a gina a Danja

Gwamna Radda ya ce karamar tashar ta Mini-Hydro 1MW za ta taimaka wa manoma rage asarar amfanin gona bayan girbi, ta hanyar samar da wuta ga injinan niƙa, sarrafawa da adanawa.

Ya ƙara da cewa aikin zai inganta tsaro, ilimi, kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a yankin, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda a wurin kaddamar da tashar samar da wuta a Danja Hoto: Chief Press Secretary
Source: Facebook

Da yake bayyana aikin Danja a matsayin na farko, gwamnan ya ce za a aiwatar da irin wannan aiki a sauran manyan dam-dam na jihar, ciki har da Zobe, Jibia, Sabke da Ajiwa.

“Burimmu shi ne amfani da albarkatun ruwanmu domin yaƙar talauci, ƙarfafa tattalin arzikin karkara da samar da ci gaba mai dorewa a faɗin Jihar Katsina," in ji shi.

Wakilin Legit Hausa ya zanta da wasu mazauna Danja a jihar Katsina kan wannan aiki, inda wasu ke yabawa gwamna, wasu kuma na ganin sai aikin ya tabbata tukunna.

Kara karanta wannan

Elon Musk ya zama mutumin farko a duniya da dukiyarsa ta haura $600bn

Wani matashi, Kabir Sulaiman ya yabi Malam Dikko Radda, yana mai cewa samar da wuta na daya daga cikin abubuwan da ke taimaka wa talakawa kai tsaye.

Ya ce matukar aka yi nasarar kammala wannan aiki kamar yadda aka tsara, mutanen karamar hukumar Danja za su amfana ta bangarori da dama.

"Na je wurin taron kuma na ji jawabin da mai girma gwamna ya yi, abin da zan ce shi ne muna masa fatan alheri, rashin wuta na daya daga cikin abubuwan da ke ci mana tuwo a kwarya.
"Muna da sana'o'i da dama da ke bukatar wuta amma dole sai dai mu nemi inji, idan wannan aiki ya tabbata, zan iya cewa Danja za ta kara samun ci gaba a fannin tattalin arziki," in ji shi.

Sai dai Hamza Ahmad ya shaida ma wakilinmu cewa wannan aiki ne mai kyau to amma wasu lokutan 'yan siyasa ba abin yarda ba ne.

Radda ya rattaba hannu a kasafin 2026

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dikko Radda ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2026 bayan Majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da shi.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya yarda matarsa, Aisha za ta kashe shi a Aso Rock Villa

Kasafin mai taken 'Building Your Future' watau gina goben al'umma zai lakume kudi har ₦897,865,078,252.05, kuma shi ne irinsa na farko a tarihin Katsina.

Da yake rattaba hannu a fadar gwamnati, Gwamna Radda ya yabawa Majalisar dokokin Katsina bisa yadda ta yi gaggawa wajen zartar da kasafin kudin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262