Akpabio Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Ofis sakamakon Rashin Lafiya? An Ji Gaskiyar Abin da Ya Faru
- Wasu rahotanni sun yadu a kafafen sada zumunta kan rashin lafiyar shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio
- Rahotannin dai sun yi ikirarin cewa rashin lafiyar Akpabio ta yi tsanani bayan ya suma, aka garzaya da shi zuwa wani asibiti a kasar waje
- Sai dai, hadimin shugaban majalisar dattawan, ya fito ya yi sharhi kan wadannan rahotannin da aka yada a kan ubangidansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan jita-jitar cewa ya kamu da rashin lafiya.
Godswill Akpabio ya karyata rahotannin da ke ikirarin cewa ya fadi ya suma kuma an dauke shi zuwa wani asibiti a birnin Landan domin jinya.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce da yake mayar da martani kan rahotannin, Mai ba shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Kenny Okolugbo, ya bayyana ikirarin a matsayin karya.
An yada jita-jita kan lafiyar Godswill Akpabio
Jita-jitar wadda ta bazu a ranar Litinin ta wasu kafafen yada labarai na intanet, ta yi ikirarin cewa an dauki Sanata Akpabio a cikin jirgin sama zuwa wani asibiti a Landan bayan ya fadi ya suma.
Lokacin da manema labarai suka tuntube shi, Okolugbo ya yi watsi da rahoton yana cewa "karya ne, labarin bogi ne,” ba tare da bayar da karin bayani ba.
Me aka ce kan rashin lafiyar Akpabio?
Wasu rahotanni sun ambato majiyoyi na cewa Akpabio ya fadi ya suma ne a ranar 10 ga wannan wata, sannan aka garzaya da shi zuwa Landan cikin wani jirgin sama da attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya samar.
A cewar wadannan majiyoyi, lamarin ya sa shugaban majalisar dattawa bai halarci wasu muhimman ayyukan hukuma ba, ciki har da taron tattaunawa kan tsarin kashe kudi na matsakaicin lokaci (MTEF) da takardar tsarin haraji (FSP) da aka gudanar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan
"Karya kake yi," Tsohon gwamnan Sakkwato ya maida martani mai zafi ga Bello Turji
Rahoton ya kara da cewa halin rashin lafiyar Akpabio ya yi tsanani har ya bukaci ci gaba da jinya a kasashen waje, yana mai cewa wannan shi ne karo na biyu da aka garzaya da shi Landan domin jinya.
Haka kuma, rahoton ya yi zargin cewa wasu sanatoci da dama sun yi tafiya zuwa Landan domin duba lafiyar Shugaban Majalisar Dattawa.

Source: Facebook
Dangane da zargin kwantar da shi jinya a kasashen ketare, an ce wasu sanatoci da dama sun tafi domin ziyartar sa.
Majiyoyin da rahoton ya ambata sun kara da cewa likitocin da ke kula da Akpabio sun ba shi shawarar rage yawan ayyukan da yake yi.
Wata majiyar ta ce likitoci sun ba shi shawarar ya sauka daga Majalisar Dattawa domin ya kula da lafiyarsa.
Sai dai duk wadannan labarai za su kasance ba gaskiya ba tun da na kusa da tsohon gwamnan na Akwa Ibom suka tabbatar da yana nan kalau.
Godswill Akpabio ya ba Peter Obi shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ba da shawara ga Peter Obi na jam'iyyar LP.
Akpabio ya shawarci Obi da ya fara warware matsalolin cikin gida a aramar jam’iyyarsa kafin ya yi burin zama shugaban kasar Najeriya.
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa idan ba zai iya magance matsalolin LP ba, to kuwa ba shi da cancantar mulkin ƙasa mai girma kamar Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

