Matar Buhari, Aisha Ta Fadi yadda Iyalansa ke Rayuwa bayan Rasuwarsa
- Aisha Buhari ta ce rayuwa ta sauya tun bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a watan Yulin 2025
- Ta bayyana cewa an rubuta littafin tarihin Muhammadu Buhari tun shekaru 10 da suka wuce kafin a sake ƙaddamar da shi
- Ta kuma karyata jita-jitar cewa Buhari wani Jibril ne daga Sudan, tana mai alakanta ta da raunin sadarwa da yada rade-radi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Bayan ƙaddamar da wani littafi da ke ɗauke da tarihin rayuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, uwargidarsa Aisha Buhari ta yi bayani kan yadda take fuskantar rayuwa a yanzu ba tare da marigayin ba.
Ta bayyana hakan ne a Abuja, inda aka gudanar da taron sake ƙaddamar da littafin da ke bayani kan rayuwar Buhari tun daga farko har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Kara karanta wannan
Yadda hadiman Buhari suka so ayyana Ahmad Lawan a matsayin dan takarar APC a zaben 2023

Source: Twitter
A bidiyon da RFI Hausa ta wallafa a Facebook, Aisha Buhari ta ce wannan lokaci ya zame mata wani sabon babi a rayuwa bayan rasuwar Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin sake ƙaddamar da littafin Muhammadu Buhari
A cewar Aisha Buhari, an rubuta littafin tarihin rayuwar Muhammadu Buhari ne tun kusan shekaru 10 da suka wuce, a lokacin da yake raye kuma yana cikin harkokin kasa.
Ta ce kwanakin baya ne aka tuntube ta aka ce ana son sake ƙaddamar da littafin a lokacin cikar shekaru 25 da kafuwar kungiyar ACF, abin da ya sa ta ga dacewar a sake duba littafin.
Uwargidar marigayin ta bayyana cewa a ganinta, akwai abubuwa da dama da suka faru bayan rubuta littafin da ya dace a ƙara, ciki har da rasuwar Buhari.
Kokarin Tinubu wajen sake buga littafin tarihin Buhari
Aisha Buhari ta ce bayan gaza kaddamar da littafin a taron ACF, ta nemi alfarma wajen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin a ba da dama a sake ƙaddamar da shi.
Ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya amince da bukatarta, aka kuma tsara sake ƙaddamar da littafin a ranar 15, Disamba, 2025.
Rayuwar iyalai bayan mutuwar Buhari
Da take magana kan halin da take ciki a yanzu, Aisha Buhari ta ce rayuwa ba za ta taba zama kamar yadda take ba tun bayan rasuwar mai gidanta.
Ta ce:
“Rayuwa ba za ta zama kamar da ba,”
Game da alaka da mutane, Aisha Buhari ta ce tun da farko ba ta saba cudanya da jama’a sosai ba, don haka a yanzu ta fi zama tare da ‘ya’yanta da jikokinta.
Ta kara da cewa mutanen da suka yi alaka da Buhari sun zo sun yi ta’aziyya, daga bisani kowa ya koma harkokinsa.

Source: Facebook
Karyata jita-jitar 'Jibril daga Sudan'
A cikin littafin da aka ƙaddamar, Aisha Buhari ta karyata jita-jitar da ta daɗe tana yawo cewa Buhari yana da wani makamanci da ake kira 'Jibrilun Sudan.'
Punch ta wallafa cewa ta bayyana wannan magana a matsayin abin dariya, tana mai cewa ba gaskiya ba ce sam-sam.

Kara karanta wannan
Bayan shekaru, an ji abin da ya hana Buhari bayyana wanda yake so ya gaje shi a 2023
An ce Aisha za ta kashe Buhari a Villa
A wani labarin, mun kawo muku cewa Aisha Muhammadu Buhari ta ce akwai lokacin da aka rika yada jita-jitar cewa za ta kashe mijinta.
A bayanan da ta yi, Aisha Buhari ta ce a karon farko Buhari ya yarda da labarin, inda ya fara sauya irin mu'amalar da yake yi.
Ta kara da cewa hakan ya jawo tsaiko game da shan magani da yanayin cin abincin shi, wanda ya yi tasiri wajen dagula lafiyarsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
