Yadda Buhari Ya Yarda Matarsa, Aisha za Ta Kashe Shi a Aso Rock Villa
- Aisha Buhari ta bayyana yadda marigayi Muhammadu Buhari ya fara kulle kansa a daki sakamakon jita-jita a fadar shugaban kasa
- Hakan na zuwa ne yayin bayani game da matsananciyar rashin lafiyar da ta kai shi jinya na kwanaki 154 a shekarar 2017 a birnin London
- Labarin ya fito ne cikin sabon littafin tarihin marigayi Buhari da aka ƙaddamar a fadar gwamnati a Abuja ranar 15 ga Disamban 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Aisha Buhari ta bayyana cewa marigayi mijinta, Muhammadu Buhari, ya taɓa yarda da jita-jitar da ake yadawa a fadar Aso Rock cewa ita ce ke shirin kashe shi, lamarin da ya jefa shi cikin fargaba na ɗan lokaci.
A cewarta, wannan jita-jita ta shafi lafiyarsa matuƙa, har ta kai ga sauya dabi’unsa, gami da fara kulle ɗakinsa da kuma lalacewar tsarin cin abinci da shan magungunan gina jiki.

Source: Twitter
Punch ta ce bayanan nata na cikin sabon littafi mai shafi 600 mai taken From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari, wanda Dr. Charles Omole ya rubuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Littafin ya kunshi babi 22 kan rayuwar Buhari tun daga Daura a jihar Katsina har zuwa rasuwarsa a wani asibiti a London a Yuli, 2025.
Yadda aka ce Aisha za ta kashe Buhari
Littafin ya ruwaito Aisha Muhammadu Buhari na bayani game da yadda aka yada cewa ta so kashe tsohon shugaban kasar:
“Sa aka yada jita-jita mai tayar da hankali. Suka ce ni na ke son kashe shi.”
Ta ƙara da cewa mijinta ya yarda da labarin na tsawon kusan mako guda kafin daga bisani ya gano lamarin ba gaskiya ba ne.
Ta bayyana cewa a wannan lokaci Buhari ya fara kulle kansa, ya sauya wasu ƙananan halaye na yau da kullum, kuma abin da ya fi muni shi ne jinkiri ko tsallake abinci gaba ɗaya, tare da dakatar da shan ƙarin sinadaran gina jiki da likitoci suka ba shi.

Kara karanta wannan
Bayan shekaru, an ji abin da ya hana Buhari bayyana wanda yake so ya gaje shi a 2023
Wannan tabarbarewar, inji littafin, ta kai ga tafiyarsa sau biyu zuwa Birtaniya domin jinya a shekarar 2017, inda ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa a wancan lokaci, Yemi Osinbajo.
Aisha Buhari ta karyata zargin kashe mijinta
Dr. Omole ya rubuta cewa Aisha Buhari ta karyata dukkan labaran da ke cewa an yi yunkurin saka guba ko makarkashiya a kan rayuwar mijinta.
Daily Post ta wallafa cewa ta bayyana cewa a London, likitoci sun ƙara masa ƙarin magungunan gina jiki masu ƙarfi. Amma da farko Buhari yana jin tsoro bai rika shan su yadda aka tsara ba.
Daga nan ne ta ɗauki alhakin kula da lafiyarsa, tana saka masa ƙarin magungunan cikin lemun kwalba ba tare da ya sani ba.

Source: Twitter
Za a kaddamar da littafin Buhari a Abuja
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad zai kaddamar da wani littafi.
Rahotanni sun nuna cewa littafin ya shafi wasu muhimman abubuwa game da tarihin aiki da ya yi da Muhammadu Buhari.
Ana sa ran cewa manyan mutane da suka hada da mai alfarma Sarkin Musulmi na cikin wadanda za su halarci taron a Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
