Wata Sabuwa: Malami Ya Yi Sababbin Zarge Zarge kan Shugaban EFCC bayan Ci Gaba da Tsare Shi
- Tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN, ya koka kan ci gaba da tsare shi da hukumar EFCC ke yi
- Abubakar Malami ya yi zargin cewa shugaban EFCC ya kullace shi saboda wasu abubuwa da suka faru a baya
- Tsohon Ministan ya ba hukumar EFCC wa'adin lokacin da za ta sake shi ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya bukaci shugaban EFCC da ya janye hannunsa nan take daga binciken da ake yi masa.
Abubakar Malami ya zargi shugaban na EFCC da nuna son kai, kiyayyar kashin kai da kuma tsangwamar siyasa da ke da alaka da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar ADC.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a kafafen yada labarai, Muhammad Doka, ya fitar a shafin Facebook ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan
Bayan ganin bidiyon Bello Turji, APC ta hango dalilin alakanta Matawalle da 'yan bindiga
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanne zarge-zarge Abubakar Malami ya yi?
Malami ya zargi EFCC da gudanar da abin da ya kira tsarewa ba bisa ka’ida ba, muzgunawa ta hanyar amfani kafafen yada labarai da kuma take hanyoyin shari’a.
Tsohon Ministan ya jaddada cewa binciken da ake yi masa ba bisa dokar aiki ba ne, sai dai sakamakon “dadaddiyar kiyayya” daga shugabancin EFCC.
“Ina fuskantar hukunci tun kafin a kammala bincike, kuma ba zan samu sahihin bincike na gaskiya da adalci ba a karkashin shugabancin EFCC na yanzu."
- Abubakar Malami
Tsohon Ministan Shari’ar ya jingina hujjojinsa da abubuwan da suka faru a lokacin da yake rike da mukamin AGF.
Malami ya ce a wancan lokacin gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bincike na shari’a karkashin mai shari’a Ayo Salami domin binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da cin zarafin mukami a cikin EFCC.
Hakazalika, ya bayyana cewa shugaban EFCC na yanzu shi ne sakataren hukumar a wancan lokaci, kuma rahoton Salami, wanda yanzu ke a bainar jama’a, ya kunshi bayanai marasa dadi a kansa.
"Binciken da ake yi a yanzu ya nuna alamun ramuwar gayya ta kashin kai."
- Abubakar Malami
Wace bukata Malami ya nema kan shugaban EFCC?
Bisa wannan dalili, Malami ya bukaci shugaban EFCC da ya janye daga binciken, tare da rokon Antoni-Janar na Tarayya, a matsayinsa na babban lauya na kasa, da ya shiga tsakani.
"Domin dawo da amincewa da martabar hukuma a idon jama’a, dole a mika wannan lamari ga wata hukumar tsaro ta daban da ta dace."
- Abubakar Malami

Source: Twitter
Abubakar Malami ya bukaci a sake shi
Haka kuma, Malami ya bukaci ko dai a gurfanar da shi a gaban kotu ko a sake shi cikin sa’o’i 24, yana mai dogaro da sassan 35 (3), (4) da (5) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa gyara).
"Kotun da ke da hurumi kadai ce ke da ikon sauraron wannan lamari bisa doka, ba wata hukuma da siyasa ta gurbata ba."
- Abubakar Malami
Ministan Buhari ya yi zargi kan EFCC

Kara karanta wannan
Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya zargi hukumar EFCC da hana shi damar samun beli.
Kwararren lauyan ya zargi EFCC da hana shi damar cika sharuddan beli da aka gindaya masa, yana mai cewa sharuddan belin sun yi tsauri kuma suna da wahalar cikawa.
Hakazalika, Malami ya kuma yi kira ga hukumar EFCC da ta yi adalci ta hanyar gabatar da sharuddan beli masu yiwuwa a cika.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
