Tinubu Ya Kadu kan Mutuwar Mataimakin Gwamna, Ya Aika Sakon Ta'aziyya
- Ana ci gaba da jimami da alhinin rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, wanda ya yi bankwana da duniya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun masu aika sakonnin ta'aziyyarsu ga gwamnati da al'ummar jihar Bayelsa kan rasuwar mataimakin gwamnan
- Mai girma Bola Tinubu ya tuna da gudunmawar da marigayi Lawrence Ewhrudjakpo ya bayar tare da yi masa addu'o'in samun rahama
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.
Shugaba Tinubu ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Bayelsa kan rasuwar marigayi Lawrence Ewhrudjakpo.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Cif Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025, wadda Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Gwamna Diri ya umarci gudanar da bincike bayan mataimakinsa ya yi mutuwar farat daya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya yi alhinin rasuwar Ewhrudjakpo
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Ewhrudjakpo a matsayin jajirtaccen mutum mai gaskiya da rikon amana, wanda ya yi wa jihar Bayelsa da Najeriya hidima cikin kishin kasa da sadaukarwa.
Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, tare da jajantawa matar marigayin, Barista Beatrice Ewhrudjakpo, ’ya’yansa, ’yan uwa, abokai da dukkan wadanda suka yi aiki tare da shi a tsawon shekarunsa na hidimar jama’a.
Shugaba Tinubu ya tuna da gagarumar gudunmawar da marigayi mataimakin gwamnan ya bayar.
Tinubu ya yaba da sadaukarwar marigayin
Mai girma Tinubu ya jaddada cewa Ewhrudjakpo ya taba rike mukamin kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa a jihar Bayelsa, kafin daga bisani a zabe shi Sanata mai wakiltar mazabar Bayelsa ta Yamma.
A cewar shugaban kasa, gudunmawar Ewhrudjakpo wajen ci gaban jihar Bayelsa ta fito karara ta hanyar ayyukan more rayuwa da ya kula da su, da kuma rawar da ya taka a fannin dokoki da tsara manufofi a lokacin da yake majalisar dattawa.

Source: Facebook
Me Tinubu ya gayawa gwamnatin Bayelsa?
Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnati da al’ummar jihar Bayelsa da su kiyaye tare da girmama abin da marigayi mataimakin gwamnan ya bari.
Har ila yau, Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya ji kan marigayin, Ya kuma ba iyalansa, gwamnatin jihar da daukacin al’ummar Bayelsa hakuri da juriya a wannan lokaci mai cike da alhini.
Diri ya umarci a binciki mutuwar mataimakin gwamna
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya koka kan rade-radi da kananan maganganun da ake yadawa kan rasuwar mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.
Gwamna Diri ya bayar da umarnin a gudanar da binciken gawa, domin gano musabbabin mutuwar mataimakin gwamnan jihar, wanda kwanakinsa suka kare a duniya.
Hakazalika, Gwamna Diri ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “yawan shirme da ake yadawa a kafafen sada zumunta” game da mutuwar Ewhrudjakpo, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a siyasantar da rasuwarsa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
