Ainihin Abin da Najeria Ta Kulla Yarjejeniyar Haraji da Faransa a kai Ya Fito daga FIRS
- Hukumar FIRS ta ce yarjejeniyar fahimta da ta kulla da hukumar haraji ta Faransa ba ta bai wa kowacce kasa damar samun bayanan ‘yan Najeriya ba
- FIRS ta jaddada cewa yarjejeniyar na da nufin musayar ilimi da kara samar da kwarewa ne kawai tsakanin kasashen, ba tare da barazana ga ikon kasa ba
- Martanin ya zo ne bayan sukar da kungiyar dattawan Arewa ta NEF da jam’iyyar adawa ta ADC suka yi, suna kira da a soke yarjejeniyar gaba daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar tattara haraji ta FIRS ta fito fili ta fayyace yarjejeniyar fahimtar juna da ta kulla da hukumar haraji ta Faransa, DGFiP.
A bayanin da ta yi, FIRS ta ce babu wani bangare na yarjejeniyar da ya bai wa kasar Faransa damar samun bayanan harajin ‘yan Najeriya.

Source: Twitter
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da martanin hukumar FIRS ne a wani sako da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.
Martanin FIRS kan yarjejeniya da Faransa
A cewar FIRS, yarjejeniyar ba ta da alaka da mika bayanan masu biyan haraji, ko bai wa wata kasa damar shiga kundin harajin Najeriya.
Hukumar ta ce duk dokokin Najeriya da suka shafi kare bayanai, tsaron yanar gizo da ikon kasa na nan daram kuma ana aiwatar da su ba tare da sassauci ba.
Ta kara da cewa hukumar NRS da za ta maye gurbin FIRS nan gaba tana daukar tsaron kasa da bayanan jama’a a matsayin muhimmin ginshiki.
Manufar yarjejeniyar da abin da ta kunsa
FIRS ta bayyana cewa irin wannan yarjejeniya abu ne da aka saba yi tsakanin hukumomin haraji a duniya domin musayar kwarewa da koyon dabaru na zamani.
A cewarta, hukumar haraji ta Faransa na daga cikin manyan hukumomi a duniya, tana da dogon tarihi da gogewa, kula da masu biyan haraji da tsarin kudin gwamnati.
Hukumar ta jaddada cewa yarjejeniyar shawara ce kawai, ba tilastawa ba, kuma dukkan ikon aiwatarwa yana hannun Najeriya.
FIRS ta ce:
“Wannan yarjejeniya ba ta bai wa Faransa damar samun bayanan haraji ko tsarinmu ba. Ta ba mu damar koyon darusa daga gogewarsu ne kawai, ba tare da tauye ikon Najeriya ba.”
Leadership ta rahoto FIRS ta kara da cewa:
“Ba gaskiya ba ne cewa yarjejeniyar za ta kawar da kamfanonin fasaha na cikin gida. Muna ci gaba da aiki kafada da kafada da ‘yan Najeriya masu kirkire-kirkire.”
Martanin jam’iyyun adawa da kungiyoyi
Kungiyar dattawan Arewa ta NEF da jam’iyyar ADC sun bukaci a soke yarjejeniyar, suna nuna damuwa kan tsaron bayanan kasa.
Jam’iyyar ADC ta ce tana goyon bayan gyaran tsarin haraji, amma hanyar da aka bi wajen cimma yarjejeniyar na bukatar karin bayani ga jama’a.

Source: Twitter
A karshe, FIRS ta ce tana maraba da muhawara da tambayoyi daga jama’a kan gyaran haraji, amma ta bukaci a duba hakikanin abin da yarjejeniyar ta kunsa.

Kara karanta wannan
Najeriya ta hada kai da Faransa a shirin fara aiki da dokar harajin Tinubu a 2026
Dangote ya rage kudin mai a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa Alhaji Aliko Dangote ya sanar da cewa an kusa fara cin gajiyar rage kudin mai da ya yi.
Ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a matatar shi da ke Legas, inda ya yi magana game da shigo da mai daga waje.
A cewar Aliko Dangote, daga ranar Talata, 16 da Disamban 2026 'yan Najeriya za su fara samun sauki bayan rage kudin mai da ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

