Rashin Tsaro: Gwamna Abba Ya Dauki Sabon Mataki don Kare Rayuka a Kano
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na ci gaba da daukar matakai na musamman domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar
- Abba Kabir Yusuf ya amince da kafa wata sabuwar runduna ta musamman wadda za ta rika sanya idanu a tashoshin motar da ake da su
- Rundunar za kuma ta yi aikin hadin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da kawar da aikata laifuffuka a fadin jihar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa rundunar tsaro ta musamman nan take.
Gwamna Abba Kabir ya amince da kafa rundunar ne domin tunkarar matsalolin tsaro a tashoshin mota da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a a fadin jihar Kano.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 14 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka kafa sabuwar rundunar?
A cewar sanarwar, wannan shiri mataki ne na rigakafi da nufin dakile barazanar tsaro tun kafin ta ta’azzara, karfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da kuma dawo da amincewar jama’a.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada matsayar gwamnatinsa ta rashin amincewa da aiakta laifuffuka, tare da ba da tabbacin cikakken goyon baya ga hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
An bayyana tashoshin mota a matsayin wuraren da ke da haɗari sosai saboda yawan zirga-zirgar jama’a, da kuma wasu sababbin abubuwan da suka shafi tsaro, ciki har da kama wasu da ake zargi da aikata laifi a tashar mota ta Kofar Ruwa.
Sanarwar ta ce rundunar ta musamman za ta gudanar da tsauraran sintiri, tattara bayanan sirri, da hadin gwiwar ayyukan tsaro a tashoshin mota da sauran wuraren da ke da rauni.
Runduar za ta rika sa ido a gidajen mai
Haka kuma, aikin rundunar zai shafi gidajen mai da sauran wuraren taruwar jama’a inda ake yawan haduwa da cunkoso.
Wannan mataki ya nuna kudurin gwamnan Kano na hana aikata laifuffuka da kuma tabbatar da tsaron jihar Kano, musamman a manyan hanyoyin shiga da fita cikin birnin Kano.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan jihar Kano
- An kashe mace mai juna biyu da jariri ɗan wata 18 a Kano, jama'a sun firgita
- Gwamna Abba ya nada mace ta farko a matsayin shugabar jami'ar gwamnati a Kano
- Gwamna Abba Kabir ya ciri tuta, an zakulo fannin da Kano ta zarce sauran jihohi
Gwamna Abba ya haramta Hisbah Fisabillahi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta haramta kungiyar Hisbah Fisabilillahi wadda Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa umarnin hannu a ranar 8, Disamba, 2025 kuma ya fara aiki nan take, tare da umartar hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa kafa wata runduna ta daban da ke dauke da siffofi irin na Hisbah na iya rushe tsarin doka da oda, tare da raunana ikon hukuma da dokar da ta kafa Hukumar Hisbah.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

