Lokaci Ya Yi: Tsohon Jakadan Najeriya, Sheikh AbdulAzeez Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Kungiyar IEDPU ta tabbatar da rasuwar tsohon shugabanta kuma tsohon jakadan Najeriya a kasar China, Sheikh Uthman AbdulAzeez
- Ambasada AbdulAzeez ya rasu ne a daren ranar Asabar bayan fama da gajeruwar rashin lafiya kuma za a yi jana'izarsa yau Lahadi
- Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki sun yi ta'aziyyar wannan rashi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara, Nigeria - Tsohon babban jami’in leƙen asiri na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA) kuma tsohon jakadan Najeriya a China, Ambasada Sheikh Uthman AbdulAzeez, ya rasu.
AbdulAzeez ya rasu yana da shekaru 71 a daren ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.

Source: Facebook
An sanar da rasuwar Ambasada AbdulAzeez
Shugaban kungiyar ci gaban masarautar Ilorin (IEDPU), Alhaji AbdulMumin AbdulMalik, ya tabbatar da rasuwar tsohon jakadan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Cikin zuciya mai nauyi da hawaye a idanuwana, nake sanar da rasuwar tsohon Shugaban Kungiyar IEDPU, Ambasada Sheikh AbdulAzeez Uthman.
“Mun rasa wannan bawan Allah bayan gajeriyar rashin lafiya a ranar Asabar. Za a yi jana’izarsa a ranar Lahadi (yau).
“Don Allah ku sanya iyalan marigayin a cikin addu’o’inku a wannan lokaci mai raɗaɗi na rashin masoyi. Allah Ya saka wa Ambasada Sheikh AbdulAzeez Uthman da Aljannatul Firdaus."
Gwamnan Kwara ya yi ta'aziyya
Da yake ta'aziyya, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana AbdulAzeez a matsayin mutum mai kyawawan ɗabi’u wanda rayuwarsa ta yi tasiri ga al’ummarsa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta ta'aziyya da sakataren yada labaran gwamnan Kwara, Rafiu Ajakaye, ya fitar yau Lahadi.
Gwamnan ya roƙi Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya shigar da shi Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalansa, abokansa da duk masu alaƙa da shi ƙarfin zuciya da haƙurin jure wannan rashi.

Source: Facebook
Bukola Saraki ya mika sakon ta'aziyya
Haka zalika, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya yi matuƙar alhinin wannan “rashi mai raɗaɗi kuma wanda ba za a iya maye gurbinsa ba.”
Ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen jami’in diflomasiyya, masani a harkokin tsaro da leƙen asiri, dattijo mai daraja, jagoran al’umma kuma ginshiƙin haɗin kai.
A wata sanarwa da jami’in yada labaransa kan harkokin cikin gida, Abdulganiyu Abdulqadir, ya sa hannu, Saraki ya ce rayuwar marigayin ta kasance cike da sadaukarwa ga Masarautar Ilorin da al'umma gaba ɗaya.
Farfesa Adamu ya rasu a Zaria
A wani labarin, kun ji cewa Farfesa Adamu Baikie, wanda shi ne mutum na farko da ya fara taka matsayin Farfesa a fannin ilimi a Arewacin Najeriya, ya riga mu gidan gaskiya.
Babban dansa, Manjo Muhammad Adamu (mai ritaya) ya ce mahaifinsu, Farfesa Adamu ya rasu ne da yammacin ranar Juma'a a gidansa da ke birnin Zaria a jihar Kaduna.
Farfesa Baikie ya kasance babban masani ne a harkoki ilimi, malami, kuma jami’in gudanarwa a manyan jami’o’i a cikin Najeriya da kasashen waje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


