An Samu Matsala: Jirgin Sama Dauke da Fasinjoji Ya Yi Hatsari a Kano
- Wani jirgin sama ya gamu da matsala a filin tashi da saukar jirage na kasa da kasa na Malam Aminu Kano
- Jirgin wanda ya taso daga birnin tarayya Abuja ya samu matsala lokacin da ya zo sauka a safiyar ranar Lahadi, 14 ga watan Disamban 2025
- Sai dai, an samu nasarar fitar da ma'aikata da fasinjojin da ke cikin jirgin saman ba tare da wata tangarda ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Wani jirgin sama mai zaman kansa da kamfanin Flybird ke kula da shi ya yi hatsari bayan ya samu matsala a Kano.
Jirgin ya sauka cikin gaggawa a filin jirgin sama na kasa da kasa na Malam Aminu Kano (MAKIA) da ke Kano.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne lokacin da jirgin, wanda ya tashi daga Abuja, ke ƙoƙarin sauka a filin jirgin saman na Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jirgin sama ya yi hatsari a Kano
Wata majiya daga filin jirgin sama ta bayyana cewa babu wani fasinja ko ma’aikacin jirgin da ya samu rauni sakamakon lamarin.
Sai dai majiyar ta ce ba ta da cikakken bayani kan abin da ya faru, tana mai cewa hukumar kula da sufurin jiragen sama da ke Legas da kuma hedkwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa (FAAN) ne kaɗai za su iya bayar da cikakken bayani.
Wata majiyar daban a filin jirgin saman ta ce mutane 11 ne ke cikin jirgin a lokacin da hatsarin ya faru.
Jirgin saman, mai lambar rajista 5N-ISB, yana kan hanyarsa ne daga Abuja zuwa Kano lokacin da ya fuskanci matsala yayin sauka a kusan karfe 9:30 na safe.
Shaidun gani da ido a filin jirgin saman sun ce jirgin ya tsaya cak a kan titin saukar jirage, kuma nan take aka fitar da fasinjojin daga cikinsa.
“An gaggauta fitar da kowa daga cikin jirgin, kuma Alhamdulillahi babu wanda ya samu rauni."
- Wani shaidar gani da ido
An tabbatar da aukuwar lamarin
Jaridar The Punch ta ce a wata sanarwa da kamfanin Flybird ya fitar a Legas, wadda sashen hulɗa da jama’a na kamfanin ya sanya wa hannu, kamfanin ya bayyana lamarin a matsayin saukar jirgi da ba a saba gani ba, yana mai jaddada cewa an bi dukkan ka’idojin tsaro.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Matukan jirgin sun bi dukkan ka’idojin aiki da tsaro da aka tanada, inda suka tsayar da jirgin cikin aminci."
Kamfanin Flybird ya tabbatar da cewa dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun sauka lafiya, kuma ba a samu wani rauni ba.

Source: Twitter
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“An killace jirgin, kuma an kai rahoton lamarin ga hukumomin sufurin jiragen sama da suka dace."
Kamfanin ya kara da cewa an fara cikakken binciken bisa ga ka’idojin da hukumomi suka tanada.
Flybird ya sake jaddada kudurinsa na tabbatar da tsaro da ingantaccen aiki, tare da yin alkawarin ba da cikakken haɗin kai ga hukumomin jiragen sama yayin da ake ci gaba da bincike.
Jirgin sojojin sama ya yi hatsari a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin saman rundunar sojojin Najeriya ya gamu da hatsari a jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin yakin sojojin ya fado kasa tare da kamawa da wuta a kusa da Karabonde, cikin Karamar Hukumar Borgu ta jihar Neja.
Matukan jirgin biyu sun tsira bayan sun yi amfani da rigar sauka ta gaggawa kafin jirgin ya fadi kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


