Matawalle: Kungiya Ta ba Tinubu Shawarar Abin da Ya Dace da Karamin Ministan Tsaro
- Ana ci gaba da kiraye-kiraye ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauke karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle daga mukaminsa
- Masu yin kiraye-kirayen dai suna yi ne bisa zargin cewa tsohon gwamnan na Zamfara yana da alaka da 'yan bindiga
- Sai dai, kungiyar NSCI ta fito ta ba Shugaba Tinubu shawarar abin da ya kamata ya yi wa karamin Ministan na tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar Northern Stakeholders Consultative Initiative (NSCI) ta sake jaddada amincewarta da karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Kungiyar NSCI ta roki Shugaba Bola Tinubu da ya bar karamin Ministan tsaron a kan mukaminsa.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran kungiyar, Yerima Shettima, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bukaci Tinubu ya bar Matawalle a kujerarsa
NSCI ta ce ci gaba da rike Matawalle a matsayin karamin Ministan tsaro yana da matuƙar muhimmanci wajen karfafa tsarin tsaron kasa, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar barazanar tsaro iri-iri.
Ƙungiyar ta bayyana cewa kwarewa da tasirin da Matawalle ke da shi, musamman a yankin Arewa, na taka muhimmiyar rawa wajen kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
NSCI ta kuma yaba da kyakkyawar alakar aiki da ke tsakanin Matawalle, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da kuma Ministan tsaro, Janar Christopher Musa.
A cewar sanarwar, wannan haɗin gwiwa tsakanin manyan shugabannin tsaron guda uku ya taimaka wajen samar da tsari mai karfi da haɗin kai, wanda ke ba da damar tunkarar matsalolin tsaro masu sarkakiya da kasar nan ke fuskanta.
Kungiyar ta nuna damuwa kan kiran da ake yi a baya-bayan nan na a cire Matawalle daga mukaminsa, tana mai cewa irin waɗannan kiraye-kirayen ba su da hujja, kuma akwai siyasa a ciki, ba batun tsaron kasa ba.
A cewar NSCI, wasu mutane ne ke kokarin tayar da wannan batu domin raunana gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Meyasa ake son Tinubu ya cire Matawalle?
Ƙungiyar ta zargi masu wannan yunkuri da neman tarwatsa haɗin gwiwar siyasa da ke goyon bayan shugaban kasa gabanin zaɓen 2027.
NSCI ta ce farin jini da goyon bayan da Matawalle ke da shi a tsakanin al’ummomin Arewa babban ginshiki ne ga gwamnati, kuma duk wani yunkurin cire shi an yi shi ne domin dakile wannan goyon baya.

Source: Original
Kungiya ta yi gargadi kan cire Matawalle
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa cire Matawalle a wannan lokaci na iya kawo cikas ga ayyukan tsaro da ake gudanarwa, tare da aika sakon rashin kwarin gwiwa ga masu ruwa da tsaki da ke mara wa shirin tsaron gwamnati baya.
Ta ce Matawalle ya nuna jajircewa wajen haɗin gwiwar hukumomin tsaro daban-daban da kuma hulɗa da al’umma, abin da ta ce ya taimaka wajen samun nasarori a yakin da ake yi da rashin tsaro.
A karshe, NSCI ta roki Shugaba Tinubu da ya yi watsi da matsin lambar ‘yan siyasa, ya kuma fifita ci gaba, daidaito da kwanciyar hankali a jagorancin tsaron kasa.
Matawalle ya kare kansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya fito ya kare kansa kan zargin alaka da 'yan ta'adda.
Bello Matawalle ya ce duk wani zargi da bai tabbata ba, bai zama zargi sai an je kotu an yi shari'a kafin sanin gaskiya.
Karamin Ministan tsaron ya Ya bukaci duk masu zarginsa kan alaka da ta'addanci su je kotu da hujjoji domin gano gaskiyar lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


