Kotu Ta Yanke wa Wasu 'Yan Najeriya 4 Hukuncin Kisa, Za a Rataye Su har Lahira
- Kotu ta yankewa wasu mutane hudu hukuncin kisa kan garkuwa da tsohon ma’aikacin ExxonMobil tare da yanke masa hannu
- Alkali ya ce gwamnati ta tabbatar da laifin wadanda ake tuhuma ba tare da shakka ba, yayin da aka wanke wasu uku saboda rashin hujjoji
- Tun da fari, shaidu sun fadawa kotu yadda wadanda aka yankewa hukunci suka sace tsohon ma'aikacin, suka karbi kudin fansa N5m
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Akwa Ibom – Wata babbar kotun jihar Akwa Ibom da ke zamanta a Uyo ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin garkuwa da mutane.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun yi garkua da wani tsohon ma’aikacin kamfanin ExxonMobil, Idongesit Demas Udom, tare da yanke masa hannu bayan karɓar kudin fansa N5m.

Source: UGC
An yanke wa mutane 4 hukuncin kisa
Channels TV ta rahoto sunayen wadanda aka yanke wa hukuncin da: Chinatu Iwe Abraham (38) daga Isiala Ngwa a jihar Abia; William ThankGod Sunday (30); Ubon Monday Ebebe (30); da Saturday Jonah Udo (43) – duk daga Idung Nneke a karamar hukumar ukanafun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta same su da laifuffuka guda uku da suka hada da haɗin baki, garkuwa da mutum, da kuma yi wa wani rauni da gangan domin nakasa, gurɓata ko lalata sassan jiki.
Mai shari’a Gabriel Ette ne ya yanke hukuncin bayan karanta shari’ar tsawon kusan awa hudu, inda ya ce ɓangaren masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin waɗanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba.
Sai dai kotu ta sallami tare da wanke mutane uku – Kingsley John Akpan (32); Etimefiok Ime Ezekiel (37); da Joseph Sunday Etim (31) – sakamakon rashin isassun hujjojin da ke danganta su da laifin.
Abin da ya faru kafin su aikata laifin
A yayin shari’ar, ɓangaren gwamnati ya gabatar da shaidu biyar ciki har da wanda aka yi wa laifin kansa, yayin da dukkan mutane bakwai da ake tuhuma suka ba da shaida don kare kansu.
Udom ya shaida wa kotu cewa al’amarin ya samo asali ne tun a ranar 20 ga Disamba, 2016, bayan wata takaddama da ta taso sakamakon yunƙurin William ThankGod Sunday na shirya wani “bukukuwan ’yan daba” karo na biyu a ƙauyen.
Dattawan ƙauyen sun ƙi amincewa da bikin bayan ganin tallar da ke nuna shan giya, taba sigari da wasannin cin abinci, suna cewa hakan zai lalata tarbiyyar matasa.
An gudanar da taro a gidan Udom, inda yake a matsayin mai kula da Gidan Sarauta da Shugaban Ƙungiyar Ci Gaban Idung Nneke, aka yanke shawarar hana bikin.
Daga bisani aka kai rahoto ga jami’in ’yan sanda na yankin Ukanafun, wanda ya tura jami’ai suka dakatar da taron, in ji rahoton Leadership.
Kotu ta ji cewa wannan mataki ya fusata William ThankGod Sunday, wanda daga baya ya dora wa Udom laifin rashin nasararsa a zaɓen shugabancin matasan ƙauye, har ya aika saƙonnin barazana ga sarkin ƙauyen.

Source: Original
Garkuwa da Udom da hukuncin kotu
Shaidu sun nuna cewa a ranar 16 ga Maris, 2017, William ThankGod Sunday ya kira taro tare da abokan aikinsa, inda suka yo hayar masu garkuwa da mutane daga jihar Abia bayan ’yan daban ƙauyen sun ƙi karbar tayin aikin saboda girman Udom a garin.
Daga bisani aka sace Udom, aka biya kudin fansa Naira miliyan biyar, sannan aka yanke masa hannu.
A yayin yanke hukunci, Mai shari’a Ette ya yanke wa kowane ɗan laifi hukuncin daurin shekaru bakwai kan haɗin baki, hukuncin kisa ta hanyar rataya kan garkuwa da mutum, da kuma daurin shekaru uku kan raunatawa da gangan.
Udom, wanda yanzu ke cikin shekarunsa na saba’in, ya halarci zaman yanke hukuncin, kuma an gan shi cikin farin ciki da kwanciyar hankali bayan ganin an yi masa adalci.
An yanke wa dan sanda hukuncin kisa
A wani labari, mun ruwaito cewa, wata babbar kotun jihar Plateau, mai zama a Jos, ta yanke wa wani jami'in ɗan sanda, mai mukamin Sajen, Ruya Auta hukuncin kisa.
Babban mai shari'a David Mann, ya yanke wa Sajen Ruya Auta hukuncin kisa ne bayan kotu ta same shi da laifin kashe wani ɗalibi jami'ar Jos, Rinji Bala, a 2020.
Mai shari'a David Mann ya ce kotun ta yi cikakken nazari kan shaidu da bayanan da bangaren gwamnati ya gabatar, tare da duba da yanayin da abin ya faru, kafin yanke hukuncin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng



