Jami'an Tsaro Sun Sake Kashe Tantirin Jagoran 'Yan Bindiga a Sokoto

Jami'an Tsaro Sun Sake Kashe Tantirin Jagoran 'Yan Bindiga a Sokoto

  • Ta'addancin wani tantirin jagoran 'yan bindiga da ya addabi mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba ya zo karshe a jihar Sokoto
  • Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka Kachalla Na'Allah bayan sun tare shi a wani yanki na karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto
  • Nasarar da jami'an tsaron suka samu ta hallaka hatsabibin dan bindigan sanya mutanen yankin cikin farin ciki da annashuwa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Gamayyar jami’an tsaro sun kashe wani shahararren jagoran 'yan bindiga mai suna Kachalla Na’Allah a jihar Sokoto.

Jami'an tsaron sun kashe Kachalla Na'Allah ne a wani gagarumin farmaki da suka kai a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto, lamarin da ya sake raunana cibiyoyin ’yan bindigan da ke addabar yankin.

Jami'an tsaro sun kashe jagoran 'yan bindiga a Sokoto
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce wata majiya mai tushe daga hukumomin tsaro ta tabbatar da cewa an harbe Kachalla Na’Allah ne har lahira a ranar Juma’a, 12 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga bayan gwabza fada a Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe jagoran 'yan bindiga a Sokoto

An harbe tantirin jagoran 'yan bindigan ne yayin da jami’an tsaro suka tare shi a tsakanin kauyukan Girnashe da Kuka Tara, a gundumar Tsabre ta karamar hukumar Isa.

Majiyar ta bayyana cewa farmakin ya gudana ne ta hannun rundunar hadin gwiwa ta ’yan sanda na Mobile Police da jami’an rundunar tsaron al'umma, tare da goyon bayan sojojin Najeriya, rahoton gazettengr ya tabbatar da labarin.

Aikin hadin gwiwar da jami'an tsaron suka yi ya kai ga samunn nasarar kashe babban jagoran na ’yan bindiga wanda ya addabi mutane.

An bayyana cewa Kachalla Na’Allah ɗan uwan shahararren jagoran ’yan bindiga ne, Ibrahim Chimmo, wanda ake zargin yana buya a yankin Dajin Sububu.

Jami'an tsaro na samun nasara kan 'yan bindiga

Majiyar ta ce wannan nasara na nuni da gagarumin ci gaba wajen tarwatsa shugabanci da tsarin aiki na kungiyoyin ’yan bindiga a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Sojoji sun toshe kofofin tsiga ga 'yan bindiga a Sokoto, an hallaka tsageru

Wannan lamari na zuwa ne ’yan kwanaki kaɗan bayan dakarun runduna ta 8 ta sojojin Najeriya sun kashe wani sanannen jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a karamar hukumar Sabon Birni.

Sojoji sun kashe tantirin dan bindiga a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A halin da ake ciki kuma, mai ba Gwamna Ahmad Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmad Usman (mai ritaya), tare da al’ummar jihar, sun jinjina wa sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa nasarorin da suke samu a yakin da ake ci gaba da yi da ’yan bindiga a jihar.

Wani mazaunin Sokoto ya yaba kan nasarar da jami'an tsaron suka samu ta kashe Kachalla Na'allah.

Usman Sani ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas nasarar da jami'an tsaron suka samu abin a yaba ne.

"Wannan abin farin ciki sosai ne kuma abin a yaba. Muna matukar jinjina musu kan wannan gagarumar nasarar da suka samu. Muna rokon Allah ya ci gaba da ba su nasara."

- Usman Sani

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan tantiran 'yan bindiga a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 4, an samu labarin rasuwar tsohon 'dan Majalisar Tarayya a Najeriya

Dakarun sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar kashe ’yan bindiga 11 tare da kwato manyan makamai da dama daga hannunsu.

Rundunar ta ce bayan ta samu sahihan bayanan sirri, tawagar jami'anta sun kaddamar da kwanton bauna mai tsari, inda aka yi artabu mai zafi da ’yan bindigan, lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka wasu daga cikinsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng