Ana Rade Radin Yakubu Gowon Ya Mutu, An Hango Tsohon Shugaban Kasa a Aso Rock

Ana Rade Radin Yakubu Gowon Ya Mutu, An Hango Tsohon Shugaban Kasa a Aso Rock

  • Tsohon shugaban ƙasa Yakubu Gowon ya halarci taron sharar fagen bukukuwan Kirsimeti a Aso Rock, ana tsaka da jita-jitar ya mutu
  • Ganin Yakubu Gowon a fadar shugaban kasa ya karyata rahotannin da ake yadawa a soshiyal midiya cewa ya mutu a Landan
  • Manyan mutane ciki har da Obasanjo, Akume da Ooni na Ife sun halarci carols, inda Gowon ya karanta darasi na farko daga Injila

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Manyan tsofaffin shugabannin Najeriya sun hallara a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock, Abuja, domin halartar wani taron Kirsimeti na Nine Lessons and Carols.

Taron addinin Kirista, wanda Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta shirya, ya samu halartar tsofaffin shugabannin ƙasa Yakubu Gowon, da Olusegun Obasanjo, da sauran manyan baki.

Kara karanta wannan

"A bayyane yake": An hango abin da Tinubu zai yi wa Shettima a zaben 2027

Yakubu Gowon ya halarci wani taro a fadar shugaban kasa ana rade radin ya mutu.
Yakubu Gowon tare da Olusegun Obasanjo sun halarci wani taro kan yara. Hoto: @OBJ_Foundation
Source: Twitter

An gudanar da wannan taron ne a ranar Juma'a, 12 ga watan Disamba, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jita-jita ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Yakubu Gowon ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, rahoton da ba a tabbatar da shi ba daga kowace hukuma.

Jita-jitar mutuwar Yakubu Gowon

A ranakun baya, wasu shafukan Facebook ciki har da Igbo TV da Otito Koro sun wallafa labaran da ke ikirarin cewa tsohon shugaban ƙasa Yakubu Gowon ya mutu a wani asibiti da ke Landan.

Otito Koro sun wallafa a shafinsu na Facebook cewa Gowon ya dade yana fama da cutar sankarar fitsari tare da rashin ci, kuma ya rasu da sanyin safiyar Asabar.

Binciken Legit Hausa ya nuna cewa babu wata kafar yada labarai mai sahihanci da ta ruwaito labarin, haka kuma babu wata sanarwa daga gwamnati ko iyalan Gowon, abin da ya nuna labarin jita-jita ne kawai.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Yakubu Gowon ya halarci taro a Aso Rock

Duk da jita-jitar da ke yawo, Yakubu Gowon ya halarci taron Nine Lessons and Carols da aka gudanar a cocin fadar shugaban kasa, Abuja.

Gowon ya karanta darasi na farko a taron, inda karatun ya mayar da hankali kan alhaki da dangantakar ɗan Adam da Allah, abin da ya kara tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya.

Taron na bana ya gudana ne karkashin taken “Emmanuel: God With Us”, wanda ke nuni da imanin Kiristoci cewa Ubangiji yana tare da bayinsa a kowane hali.

Ganin Yakubu Gowon a fadar shugaban kasa ya karyata jita-jitar mutuwarsa.
Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon yana jawabi a wani taro. Hoto: @ArcSadam
Source: Twitter

Oluremi Tinubu da jagororin addini sun yi jawabi

Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta karanta darasi na tara daga Littafin Yohanna 1:1–14, inda aka jaddada imanin Kirista game da zuwan Almasihu a matsayin Kalmar Ubangiji da ta zama mutum.

Babban limamin cocin Methodist na Najeriya, Oliver Aba, ya yi huduba inda ya bukaci ’yan Najeriya su rungumi hidima ba tare da son kai ba, su kuma rumgumi haɗin kai da son kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume da Oshiomhole sun gwabza a majalisa kan tantance Omokri

Ya bayyana cewa Ubangiji yana tare da al’umma a lokutan wahala, tsadar rayuwa, matsalolin tsaro da kuma rarrabuwar kai da ake fuskanta a kasar, in ji rahoton Punch.

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Opeyemi Bamidele, da mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu.

'Abin da ya jawo yakin basasa' - Gowon

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon, ya bayyana dalilin da ya sa yarjejeniyar Aburi ta rushe, sannan yakin basasa ya barke a 1967.

Gowon ya ce sabanin da ya kunno kai tsakaninsa da Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ya ta’allaka ne kan "wanda zai rike iko da dakarun soja a yankuna".

Tsohon shugaban kasar ya ce an cimma matsaya a taron Aburi da aka yi a Ghana, amma daga baya Ojukwu ya bukaci cikakken ikon mulki na yankuna, wanda gwamnati ta ki yarda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com