An Kaddamar da Shirin YouthCred, Matasa Za Su Iya Samun Naira Miliyan 5 a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin YouthCred, wanda aka kirkira domin bai wa matasa masu aikin yi rancen kudi
- A kwanakin baya, shirin ya fara da matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) amma yanzu an bude ga kowane matashi mai aikin yi
- Ministan Kudi da Harkokin Tattalin Arziki, Wale Edun ya ce an samar da wannan shirin ne domin taimaka wa matasa su cika burikansu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shirin bai wa matasa lamuni mai suna ‘YouthCred’, ƙarƙashin Hukumar Ba da Bashin Kudi ta Najeriya (CREDICORP).
A ƙarƙashin wannan shiri, matasan Najeriya masu aikin yi da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 39 za su iya samun bashi har zuwa Naira miliyan 5.

Source: Twitter
An kaddamar da shirin YouthCred
Ministan Kuɗi da Harkokin Tattalin Arziƙi na Ƙasa, Wale Edun, ne ya jagoranci kaddamar da shirin a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Da yake jawabi a wurin, ya ce shirin wata alama ce da ke nuna hangen nesan Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen gina tattalin arziƙi na zamani da ke bai wa jama’a damar samun bashi.
Edun ya ce yayin da sauye-sauyen da gwamnati ke yi ke ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasa, ya zama dole ‘yan Najeriya su fara jin amfanin hakan kai tsaye a rayuwarsu ta yau da kullum.
Ministan ya ce hakan zai samu ne kadai ta hanyar samun kayan aiki da za su ƙara musu ƙwarewa da kwanciyar hankali a harkokin kuɗi, kamar yadda Premium Times ta kawo.
Amfanin shirin YouthCred ga matasa
Ya ce shirin YouthCred na nuni ga matakin da aka dauka wajen faɗaɗa haɗin kai a harkokin kuɗi da kuma rage matsin tattalin arziƙin da matasa masu aiki ke fuskanta.
Ministan ya ƙara da cewa shirin ya dace da manyan sauye-sauyen tattalin arziƙin da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa, waɗanda ke da nufin inganta rayuwar al’umma da kuma tallafa wa ƙananan kasuwanci da waɗanda ke tasowa.

Kara karanta wannan
Bakin Wike ya jefa shi a tasko, ana so ya biya Naira biliyan 40 kan sukar dan siyasa

Source: Twitter
Wale Edun ya ce:
“Shirin YouthCred na ku ne, mutunci ne a gare ku, ‘yancin ku na kuɗi, da damar samun jali domin ku cimma burinku ba tare da takurawa ba.
“Damar tana buɗe ga kowa, babban burin gwamnati shi ne gina tattalin arziƙi mai gasa wanda ke bunƙasa cikin sauri, kuma zai jawo kowa, matasa, mata, har ma da waɗanda ba su da galihu.
Shettima ya kaddamar da shirin NJFP 2.0
A wani rahoton, kun ji cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya kaddamar da shirin NJFP 2.0 a ranar Laraba, 22 ga Oktoba, 2025 a Abuja.
Zagaye na biyu na shirin yana da nufin samar da aƙalla guraben ayyuka 20,000 a kowace shekara, tare da bai wa matasa masu karatun digiri damar koyon aiki.
A matakin farko, sama da matasa 14,000 ne suka amfana ta hanyar horo na watanni 12, wanda ya taimaka musu wajen samun gogewa da damar aiki na dindindin.
Asali: Legit.ng
