"Ba Ka Cika Sharudda 5 ba," EFCC Ta Maida Martani, Ta Yi Kaca Kaca da Malami
- Hukumar EFCC ta musanta ikirarin da tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya yi cewa ta sanya siyasa a binciken da take masa
- Tun farko, Malami ya yi ikirarin cewa EFCC ta soke belin da ta ba shi saboda ya halarci wani gangamin siyasa a jihar Kebbi
- Sai dai EFCC ta ce wannan magana ba gaskiya ba ce, har yanzu tsohon ministan bai cika sharudda biyar da aka gindaya masa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ce tsohon Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami, bai cika sharuddan beli da aka gindaya masa ba har yanzu.
Hukumar EFCC na mayar da martani ne ga ikirarin Malami cewa an soke belinsa saboda halartar wani taron siyasa a Jihar Kebbi.

Source: Twitter
The Cable ta rahoto cewa ana binciken Malami, tsohon ministan shari'a kan tuhume-tuhume guda 18 da suka haɗa da safarar kuɗi, amfani da mukami ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma tallafa wa ta’addanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane ikirari Abubakar Malami ya yi?
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mohammed Bello Doka, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce tsohon Antoni-Janar bai karya ko gazawa wajen cika wani sharadin beli ba.
Ya ce,
“Don kauce wa ruɗani, Abubakar Malami, SAN bai gaza cika wani sharadin beli ba. EFCC ce ta soke belinsa bayan ya halarci wani taron siyasa a Jihar Kebbi, ba wai saboda ya ƙi ko ya kasa bin wani sahihin sharadi ba.”
EFCC ta maida martani ga Malami
Sai dai a wata sanarwa da EFCC ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta bayyana wannan ikirari a matsayin ƙarya.
EFCC ta ce:
“Beli wata dama ce ta wucin gadi da ake bayarwa bisa yardar hukuma domin sakin wanda ake bincike a kan wasu sharudda, har zuwa kammala bincike da gurfanarwa a kotu.
“Bisa wannan dalili, bayan an yi masa tambayoyi na ɗan lokaci a ranar 28 ga Nuwamba, 2025, an ba Malami beli na wucin gadi wanda ya dogara da sharudda guda biyar. Har zuwa yanzu bai cika ko ɗaya daga cikin waɗannan sharudda ba, kuma ba shi da niyya.
“An buƙaci ya dawo domin ci gaba da bincike a ranar 1 ga Disamba, 2025, amma abin mamaki, tsohon Ministan ya rubuto wasiƙa a ranar 4 ga Disamba, 2025 yana roƙon a masa uzuri saboda rashin lafiya.
EFCC ta nesanta kanta da siyasa
Hukumar EFCC ta ƙara da cewa Malami bai gabatar da rahoton likita ko wata sahihiyar hujja da ke nuna rashin lafiyarsa ba.
“Saboda haka, an sake gayyatarsa a ranar 8 ga Disamba, 2025 domin ci gaba da tambayoyi, kuma aka tsare shi har sai ya cika sharuddan belin da ke saura.
“A bayyane yake cewa ikirarin tsohon Ministan cewa EFCC ta soke belinsa ba shi da tushe.
"Irin waɗannan ikirari marasa tushe daga tsohon babban jami’in shari’a na ƙasa abin mamaki ne, domin EFCC ba ta da wata sha’awa kan jam’iyyar siyasar da wanda ake bincike yake ciki. Hukumar ba ta tsoma baki a siyasa."

Source: Twitter
A karshe, EFCC ta shawarci Malami da ya mayar da hankalinsa wajen cika sharuddan belin guda biyar da ya amince da su kuma ya sanya hannu a kansu a ranar 28 ga Nuwamba, 2025, in ji Leadership.
ADC ta caccaki hukumar EFCC
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar hadaka ta bayyana soke belin Abubakar Malami da EFCC ta yi a matsayin wani yunkuri na ruguza shirinsa na siyasa a jihar Kebbi.
A cewar ADC, matakin da EFCC ta dauka na nuna tana taimaka wa gwamnati wajen kokarin mukushe 'yan adawa a kasar nan.
Jam’iyyar ADC na tare da Malami wanda take ganin ba shi da laifi har sai wata kotu mai hurumi ta tabbatar da laifinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


