Ministan Sadarwa Ya Fadi Me Ya Sa ba a Kama 'Yan Bindiga Masu Kira da Waya
- Ministan sadarwa ya bayyana cewa ’yan bindiga na amfani da wata fasaha ta musamman wajen yin kira ba tare da jami’an tsaro sun gano su ba
- Gwamnatin tarayya na shirin inganta tauraron dan Adam da hasumiyoyin sadarwa domin ƙarfafa sa-ido kan harkokin tsaro a fadin Najeriya
- Bosun Tijani ya ce rashin wadatattun hasumiyoyi ya bai wa masu aikata laifi damar fakewa a yankunan da ba su da sadarwa a fadin kasar nan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja — Ministan sadarwa, Bosun Tijani, ya ce ’yan bindiga da ke addabar wasu sassan ƙasar nan na amfani da wata fasaha ta musamman wajen yin kira domin kauce wa bin diddiginsu da hukumomin tsaro ke yi.
Ministan ya ce sa-ido kan kiran wayar ’yan bindiga ya fi rikitarwa fiye da yadda yawancin ’yan Najeriya ke zato, saboda dabarun fasaha da suke amfani da su.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Seun Okinbaloye a shirin Politics Today na Channels TV a daren Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ’yan bindiga ke kira da waya
Bosun Tijani ya bayyana cewa ’yan bindigar ba sa amfani da hasumiyoyin sadarwa na yau da kullum wajen yin kira, lamarin da ke sa jami’an tsaro su kasa gano inda sakonnin su ke fitowa.
A cewarsa, suna juyar da kira daga hasumiyar sadarwa zuwa wata domin ruɗar da duk wani yunƙurin sa-ido da hukumomi ke yi a kansu.
Ya ce wannan ne ya sa suka fi zama a yankunan da ba su da isasshen sadarwa, inda ake samun gibin hasumiyoyin wayar tarho.
Za a zuba jari a hasumiyoyin sadarwa
Ministan ya ce shugaban ƙasa ya matsa lamba a zuba jari a gina hasumiyoyin sadarwa a yankunan da ke fama da matsalar tsaro, bayan an gano irin fasahar da ’yan bindiga ke amfani da ita.
A cewarsa, fahimtar wannan matsala ce ta sa gwamnati ta fahimci muhimmancin cike gurbin yankunan da ba su da na'urorin sadarwa, domin rage fakewar masu aikata laifi.
Tijani ya jaddada cewa wadatattun hasumiyoyi za su taimaka wajen sauƙaƙa tattara bayanan sirri da bin diddigin kiran waya.
Najeriya za ta inganta tauraron dan Adam
Bosun Tijani ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na aiki kan inganta tauraron dan Adam na ƙasar nan domin ƙarfafa sa-ido daga sararin samaniya.
Ya ce koda hasumiyoyin sadarwa ba su yi aiki yadda ya kamata ba, to tauraron dan Adam zai taimaka wajen cike gibin da ake da shi.
A cewarsa, ƙarfafa hasumiyoyi da tauraron dan Adam zai inganta sa-ido da kuma taimakawa hukumomin tsaro wajen gano motsin masu aikata laifi.

Source: Facebook
Ya kwatanta Najeriya da ƙasar China, inda ya ce China na da sama da hasumiyoyin sadarwan 5G miliyan hudu, yayin da Najeriya ke da hasumiyoyi 40,000 kacal.
A cewarsa, wannan bambanci na nuna dalilin da ya sa ya zama dole Najeriya ta ƙara zuba jari domin magance matsalar tsaro.
An bukaci Bello Turji ya mika wuya
A wani labarin, kun ji cewa wata kungiyar mata a Arewa maso Yamma ta yi kira ga shugaban 'yan ta'adda, Bello Turji ya mika wuya.
Matan sun bayyana haka ne yayin wani taron addu'a ga Arewa ta Yamma, Najeriya da dakarun sojojin kasar nan a Abuja.
Mai magana da yawun matan ta ce lokaci ya yi da ya kamata Bello Turji ya ajiye makamai, musamman bayan kashe mataimakinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


