Zargin Kisan Kiristoci: Shugaba Tinubu Ya Fayyace Gaskiyan kan Matsalolin Najeriya

Zargin Kisan Kiristoci: Shugaba Tinubu Ya Fayyace Gaskiyan kan Matsalolin Najeriya

  • Ana ci gaba da kai ruwa rana kan zargin da wasu ke yadawa na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya
  • Shugaban kasa Bola Ahmed ya sake fitowa ya yi magana kan zarge-zargen wadanda suka jawo Amurka ta taso Najeriya a gaba
  • Mai girma Tinubu ya nuna cewa matsalolin rashin tsaron da ake fuskanta a kasar nan ba su da alaka da addini

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake tsokaci kan zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa babu kisan kare dangi kan Kirista ko Musulmi a Najeriya.

Tinubu ya musanta zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron Nasrul-Lahi-l-Fatih Society (NASFAT) a birnin Abuja a Juma'a, 12 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sheikh Zakzaky ya dauki zafi, ya kausasa harshe kan gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Tinubu ya samu wakilcin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi.

Bola Tinubu ya musanta tsangwamar Kiristoci

Shugaba Tinubu ya ce matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar nan ba na addini ba ne, illa dai ta’addanci ne da ya samo asali daga laifuffuka, tsattsauran ra’ayi da matsalolin tarihi da tattalin arziki.

Tinubu ya ce gwamnati na aiki tukuru don shawo kan kalubalen matsalolin tsaron da suka addabi kasar nan.

“A 'yan kwanakin nan gwamnatin tarayya da mutane masu kishin kasa sun sha yakar wadannan zarge-zarge marasa tushe."
"Wadannan ikirari karya ne kuma masu hadari saboda suna iya tayar da fitina su karya zaman lafiya da hadin kanmu a matsayin kasa.”
“Najeriya ta mayar da martani cikin natsuwa. Mun jaddada cewa ba mu da wata manufa ko mataki da ke nuna wariya ko tsangwama ga wani addini.”

- Shugaba Bola Tinubu

Me Tinubu ya ce kan rashin tsaro?

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Yadda Abdullahi Ramat ya rasa kujerar shugabancin hukumar NERC

Shugaba Tinubu ya ce matsalolin tsaro suna da alaka da tarihi, tattalin arziki da laifuffuka, ba addini ba, jaridar PM News ta dauko labarin.

“Musulmi da Kiristoci duka sun kasance wadanda ta’addanci ya rutsa da su a Najeriya. Musulmi da Kiristoci duka sun tsaya tare sun yi Allah wadai da tashin hankali daga kowanne bangare."
“A matsayina na shugaban kasa, ina sake nanatawa da cikakken nauyin da kundin tsarin mulki ya dora a kaina cewa babu kisan kare dangi na Kirista a Najeriya, babu kuma kisan kare dangi na Musulmi a Najeriya. Abin da muke da shi shi ne ta’addanci da laifuffuka da tsattsauran ra’ayi.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya ce ba a yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya
Mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Wane kokari gwamnatin Najeriya ke yi?

Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kare hadin kai, ’yancin addini, da tsaron rayukan ’yan kasa.

Bola Tinubu ya karbi mulki ne a Mayun 2023 bayan nasarar tikitin Musulmi da Musulmi a zaben kasar.

“Dole mu ki duk wani labari ko magana da za ta raba mu. Ba za mu bari wani daga ciki ko waje ya jefa mana fitina ko ya fadi abin da ba gaskiya ba ne kan kasar mu ba.”

Kara karanta wannan

Jami'in kwastam da ya yi fatali da cin hancin $50,000 ya samu karin girma

- Shugaba Bola Tinubu

Rashin tsaro: Ndume ya yabawa Gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya kwararo yabo ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Ali Ndume ya yabawa shugaban kasar ne kan matakan da ya dauka don magance matsalar rashin tsaro.

Hakazalika ya ce matakan da shugaban ƙasa ya ɗauka a cikin 'yan makonnin da suka gabata wajen dakile barazanar tsaro sun fara haifar da sakamako mai gamsarwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng