Farashin Abinci Ya Ruguzo, an Fadi Jihohin da Kaya Ya Fi Araha a Najeriya

Farashin Abinci Ya Ruguzo, an Fadi Jihohin da Kaya Ya Fi Araha a Najeriya

  • Farashin wasu muhimman kayayyakin abinci a Najeriya ya yi ƙasa a watan Oktoban, 2025, a cewar sabon rahoton NBS
  • Rahoton ya nuna raguwar farashin wake, garin kwaki, tumatur da shinkafa, sai dai albasa da nama sun yi tsada a watan
  • An kuma bayyana bambancin farashin kayayyaki tsakanin jihohi da jihohi, da kuma yankuna daban-daban na ƙasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta sanar da cewa farashin kayayyakin abinci ya ragu a watan Oktoban 2025, bisa sabon rahoton da ta fitar a Abuja.

Rahoton ya kwatanta farashin abinci a watan Oktoban 2025 da na shekarar da ta gabata da kuma na watan Satumban 2025.

Masu sayar da abinci a kasuwa
Mutane sun kasa kayan abinci a kasuwa. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Punch ta rahoto NBS ta ce raguwar farashin ta fi bayyana a wake, garin kwaki, tumatur da shinkafa, duk da cewa wasu kayayyaki musamman albasa da nama ba su sauko ba.

Kara karanta wannan

DSS ta saki mutum 3 bayan kuskuren zargin ta'addanci, ta ba su diyyar N3m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana inda farashin ya fi tsada da kuma inda ya fi rahusa a kowane yanki, lamarin da ke nuna sauyin yanayi da hanyoyin sufuri.

Farashin abinci ya ragu a Oktoban 2025

A cikin bayanan da NBS ta fitar, an ce farashin mudun wake ya ragu da 37.09% daga N2,798.50 a watan Oktoba 2024 zuwa N1,760.53 a watan Oktoban 2025.

Lura da saukar farashin tsakanin watan Satumba da Oktoba kuma, farashin ya ragu da 1.74% daga N1,815.76 na Satumba.

Garin kwaki kuma ya ragu da 29.33% a a Oktoban 2025, inda ya sauka daga N1,198.05 zuwa N846.69.

Tumatur ya sauƙa da 13.43% a Oktoban 2025, daga N1,465.99 zuwa N1,269.17, yayin da ragin da aka samu tsakanin Satumba da Oktoba ya kai 0.83%.

Mudun shinkafar gida ya ragu da 2.01% a Oktoban 2025 idan aka kwatanta da 2024, daga N1,944.64 zuwa N1,913.78.

Kayan da farashinsu ya tashi a karshen 2025

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Benin bayan fatattakar sojoji masu yunkurin juyin mulki

Rahoton ya nuna cewa albasa ta tashi da 4.66% a Oktoban shekarar 2025 daga N1,251.52 zuwa N1,368.32.

Kilon Nama ya tashi da 16.93% daga N5,858.58 zuwa N6,850.51 a Oktoban 2025, sannan ya ƙaru da 0.16% daga Satumba zuwa Oktoban 2025.

Yanayin farashin kaya a jihohin Najeriya

A nazarin jihohi, Imo ce ta fi tsadar wake da farashin mudu a N2,174.09, yayin da Yobe ta fi rahusa da N1,263.68.

Rahoton Nairametrics Bayelsa kuwa ta fi tsadar garin kwaki da kudin mudu ya kai N1,165.3, jihar Plateau ce ta fi rahusa da N490.1.

Wata kasuwa da ake sayar da kayan abinci
Yadda aka sayar da kayan abinci a wata kasuwa. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Jihar Ebonyi ta fi tsadar tumatur a Najeriya da N2,148.04, yayin da jihar Plateau ta fi rahusa da N687.09.

Rahoton ya kara da cewa jihar Ogun ta fi tsadar shinkafa da N2,163.23, sai kuma Yobe ta fi rahusa da N1,523.47.

A nazarin yankuna, Kudu-maso-Gabas da Kudu-maso-Yamma suka fi tsadar wake, yayin da Arewa-maso-Yamma ta fi rahusa.

NBS ta ce shinkafa ta fi tsada a Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yamma, amma ta fi rahusa a Arewa maso Gabas

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa Fulani makiyaya da harbi, an sace shanu 168 a Filato

Farashi ya yi kasa ana shirin shiga 2026

A wani labarin, mun kawo muku cewa farashin kayan abinci ya sauka a yankuna da dama na Najeriya ana shirin shiga 2026.

Bayanan da Legit Hausa ta tattaro ya sun nuna cewa duk da saukin farashi da ake samu a yankuna, tsakar kudin sufuri na cigaba da zama kalubale.

Wasu masana tattalin arziki na ganin cewa saukar farashin zai taimaka wajen yin bukukuwan karshen shekara cikin sauki a bana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng