Minista Ya Yi Karar Malami bayan Ya 'Bukaci' N150m domin Ba Shi Kujerar Gwamna

Minista Ya Yi Karar Malami bayan Ya 'Bukaci' N150m domin Ba Shi Kujerar Gwamna

  • Ministan makamashi, Bayo Adelabu, ya zargi malamin addinin Kirista da neman karbar makudan kudi a gare shi
  • Adelabu ya zargi Elijah Ayodele da neman N150m domin ya taimaka masa zama gwamnan Oyo
  • Adelabu ya kai kara ga DSS da ‘yan sanda, yana zargin limamin da yunkurin tada fitina, annabcin karya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan makamashi, Bayo Adelabu, ya zargi Fasto Elijah Ayodele da yunkurin damfararsa.

Adelabu ya ce Ayodele ya nemi ya karɓi N150m da kuma wasu kayayyaki domin ya yi masa addu’o’in da za su tabbatar ya zama gwamnan Jihar Oyo.

Minista ya kai karar Fasto Ayodele kan takarar gwamna
Ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu. Hoto: Adebayo Adelabu.
Source: Twitter

An kai karar Fasto DSS kan zargin damfara

Hakan na cikin wata takarda da mai magana da yawun ministan, Bolaji Tunji, ya sanyawa hannu, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin takardar, an kai koke ga hedkwatar DSS domin bincikar limamin kan neman damfara da annabtar karya.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Adelabu, wanda ya taba takarar gwamna sau biyu, ya riga ya bayyana niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2027.

A cewar ministan, Ayodele ya rika aiken sakonni da zarge–zarge bayan ya ƙi bin bukatunsa.

Sakonnin da aka gani sun nuna limamin yana bukatar tutocin APC guda 24 da kuma kayan kiɗa 1,000, wadanda jimillarsu ke kai wa N50m zuwa N130m gwargwadon inganci.

Ayodele ya dage cewa umarnin da ya ke bai wa ministan daga Allah ne, yana kuma cewa Adelabu zai zama gwamna muddin ya bi umarnin.

Ya bukaci ministan ya kula sosai da karanta addu’o’i, yana kuma cewa “ba ya son ya ga ya fadi zabe."

Ana zargin Fasto da neman N150m daga minista kan takarar gwamna
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu da Fasto Elijah Ayodele. Hoto: Primate Elijah Ayodele, Adebayo Adelabu.
Source: Facebook

Minista ya yi watsi da tsafi a takararsa

Sai dai ministan ya ce ba zai iya biyan wannan kudaden ba, daga baya limamin ya fito a coci yana cewa Adelabu ya gaza kuma ba zai taba zama gwamna ba.

An ce Ayodele ya nemi ministan ya same shi idan yana da damuwa, ya kara cewa sakonninsa “gargaɗi ne daga Allah”.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume da Oshiomhole sun gwabza a majalisa kan tantance Omokri

A takardar korafi ga DSS, Adelabu ya ce burinsa na siyasa yana kan gaskiya ne da hidima, ba kan tsafi ko wani abu na ruɗani ba.

Ya bukaci DSS ta binciki limamin saboda damfara, sharri da yada annabcin karya, tare da tilasta masa janye maganganun da ya yi a bainar jama’a.

Abin da Fasto Ayodele ya ce kan zargin

A martaninsa, Ayodele ya musanta dukkan zarge-zargen, ya ce Adelabu ne ya fara neman shi, kuma shi bai taba karɓar kudi daga gare shi ba.

A cewarsa:

“Ban nemi ya ba ni kudi ba. Na sanar masa abubuwan da suka shafi aikin addini, bai yarda ba. Ni ba matalauci ba ne, ba kuma mu’amala muke yi don ya ci amanata ba.”

An bukaci korar ministan wuta a Najeriya

Kun ji cewa matasa sun buƙaci a kori ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu da shugaban kamfanin rarraba wuta na ƙasa TCN.

Ƙungiyar matasan NYTGG ta ce akwai sakaci a yawan lalacewar babban layin lantarki wanda ya samu matsala sau uku a mako guda.

A cewar kungiyar, rashin wuta ya jefa ƴan Najeriya cikin duhu, ƴan kasuwar da ke amfani da lantarki sun tafka asara mai yawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.