Sanata Marafa Ya Yi Wa Matawalle Shagube, Ya Tona Taimakon da Ya Yi Masa a Baya

Sanata Marafa Ya Yi Wa Matawalle Shagube, Ya Tona Taimakon da Ya Yi Masa a Baya

  • Sanata Kabiru Marafa ya fito ya kausasa harshe a cikin kalaman da ya yi wa karamin ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle
  • Tsohon gwamnan ya fito ya musanta ikirarin cewa Matawalle ya taba taimakonsa lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar Zamfara
  • Kabiru Marafa ya bayyana cewa sabanin hakan, shi ne wanda ya yi wa Matawalle taimakon da ba zai manta da shi ba

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Sanata Kabiru Marafa ya soki karamin Ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle, bisa ikirarin da ya yi cewa ya taimaka masa lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara.

Sanata Marafa ya ce sabanin hakan, shi ne ya goyi bayan Matawalle har Allah ya ba shi nasarar zama gwamna a 2019.

Sanata Marafa ya caccaki Bello Matawalle
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da Sanata Kabiru Marafa Hoto: Dr. Bello Matawalle, Sen Kabiru Marafa
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Marafa Support Group, Alhaji Surajo Garba Maikatako, ya fitar.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume da Oshiomhole sun gwabza a majalisa kan tantance Omokri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marafa ya karyata Matawalle

Ya bayyana cewa ikirarin da Matawalle ko shugaban APC na jiha, Tukur Danfulani, ke yi cewa sun taimaka wa Sanata Marafa, karya ce tsagwaronta.

Alhaji Surajo Garba Maikatako ya tambayi yadda Danfulani ya samu karfin gwiwa da har ya nemi a nuna inda Sanata Marafa ya taba taimakawa Matawalle.

“Wannan jujjuya gaskiya ne. Mu ne ya kamata mu tambayi inda Matawalle ya taɓa taimaka wa Sanata Marafa.”

- Alhaji Surajo Garba Maikatako

Wane taimako Marafa ya yi wa Matawalle?

A cewarsa, tarihin siyasar Zamfara ya nuna cewa Sanata Marafa ne ya taimaka wa Matawalle ya zama gwamna, kuma Matawalle ma ya taba tabbatar da hakan, yana mai cewa ba zai taɓa cin amanarsa ba, amma yanzu ya karya wannan alƙawari.

“Sanata Marafa ne ya kafa dukkan gwamnatin Bello Matawalle. Matawalle ya san haka, kuma ya yi alkawarin ba zai taba cin amanarsa ba, amma yanzu ya saba alkawari."

Kara karanta wannan

Jami'in kwastam da ya yi fatali da cin hancin $50,000 ya samu karin girma

- Alhaji Surajo Garba Maikatako

Maikatako ya bayyana ikirarin Danfulani cewa mutane na kishi ko yi musu hassada a matsayin abin dariya.

“Ta yaya za mu yi kishin abin da mu muka kirkiro? Mu ne tushen su. Idan wata nasara ce, mu muka samar da ita, su kuwa sakamakon mu ne.”
“Tukur Danfulani da ubangidansa Bello Matawalle sun gaza. Sun gaza a siyasa, a dabi’a, kuma yanzu a tarihi. Sun gaza cika alƙawari, sun gaza bin gaskiya, kuma yanzu ma sun kasa faɗin gaskiyar asalinsu.”

- Alhaji Surajo Garba Maikatako

Sanata Kabiru Marafa ya yi kalamai kan Matawalle
Tsohon sanata Kabiru Marafa a zauren majalisar dattawa Hoto: Sen Kabiru Marafa
Source: Facebook

Sanata Marafa zai ci gaba da fadin gaskiya

A karshe, Maikatako ya ce yayin da Sanata Marafa ke ci gaba da faɗin gaskiya ba tare da tsoro ba, tsohon abokinsa kuma yana fuskantar zarge-zarge masu nauyi daga ingantattun majiyoyi da ya kasa kai wa kotu don kare kansa.

“Mutanen Zamfara sun riga sun gane gaskiya."

- Alhaji Surajo Garba Maikatako

Matawalle ya magantu kan masu sukarsa

Kara karanta wannan

Matawalle ya nemo wa Najeriya mafita, ya gana da Saudiyya kan lalacewar tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa karin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya fito ya yi magana kan masu sukarsa.

Matawalle masu sukarsa na yin haka ne kawai domin biyan bukatun kansu saboda sauyin matsalar tsaro da ake samu.

Karamin Ministan ya ce ya ce yana fuskantar jerin hare-haren kalaman baki, da ake yi da nufin nuna gazawarsa da kuma adawa da kokarin da yake yi na magance matsalar tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng