Sanata Ndume da Oshiomhole Sun Gwabza a Majalisa kan Tantance Omokri
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa majalisa ta rikice da hayaniya yayin tantance sababbin jakadu da Bola Tinubu ya tura
- An ce an samu zazzafar muhawara tsakanin Sanata Ali Ndume da Adams Oshiomhole yayin tantance jakadun
- Rigimar ta ɓarke ne bayan sabani kan yadda za a yi wa Reno Omokri tantancewa, duk da cewa dukkaninsu suna goyon bayan nadin nasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An samu hayaniya a Majalisar Dattawa bayan Sanata Ali Ndume da tsohon shugaban NLC, Sanata Adams Oshiomhole sun kaure da cacar baki.
Majiyoyi sun ce sanatocin sun yi wa juna zafafan maganganu yayin zaman tantance sababbin jakadu da aka tura domin amincewa.

Source: Facebook
Hatsaniya ta faru a majalisar dattawa
Hatsaniyar ta faru ne a gaban kwamitin harkokin ƙasashen waje da Sanata Sani Bello ke jagoranta, wanda ke da alhakin gudanar da tantancewar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rigimar ta ɓarke lokacin da aka kira tsohon mai taimakawa shugaban ƙasa, Reno Omokri, domin a fara tambayarsa.
Da Reno Omokri ya gabatar da kansa, Sanata Ndume ya nemi kwamitin ya bar shi ya duka domin ya wuce kawai, amma Oshiomhole ya ce dole ne ya yi magana duk da cewa biyun suna goyon bayansa.
Sanata Ndume ya nuna rashin jin daɗi kan yadda Oshiomhole ya katse shi, lamarin da ya rikide zuwa munanan zarge-zarge a bayyane.
Oshiomhole ya tuna masa cewa ya yi gwamna sau biyu, amma Ndume bai taba zama gwamna ba, abin da ya kara tayar da jijiyoyin wuya.
Daga bisani, Oshiomhole ya yaba wa Omokri, yana cewa Shugaba Tinubu ya nuna dattako domin zaben mutumin da ya taba sukar sa a baya, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ya ce:
“Gaskiya Shugaba Tinubu ya nuna halayen jagora; ko ka zage ni a baya ba yana nufin ba zan iya naɗa ka ba.”

Source: Twitter
Yadda aka shiga tsakanin Ndume, Oshiomhole
Daga bisani, sauran sanatoci, ciki har da shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, su shiga tsakani domin kwantar da tarzoma.
Daga ƙarshe Omokri ya duka ya wuce ba tare da matsala ba duk da samun korafi kan haka tun farko.
Sauran wadanda suka samu tantancewar gaggawa sun hada da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, Sanata Ita Enang; tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu; tsohon hafsan soji, Abdulrahman Dambazau; da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, da wasu tsofaffin gwamnonin jihohi.
Kwamitin zai mikawa majalisa rahoton karshe cikin 'yan kwanaki, yayin da aka turo sunayen mutum 68 daga shugaban kasa domin neman amincewar majalisa.
An samu hatsaniya a majalisar dattawa
A baya, an ji cewa zaman tantance jakadun Bola Ahmed Tinubu ya rikice bayan wanda aka turo sunansa daga Ekiti ya gaza kiran sunayen.
Sanatocin jiharsa da ke zauren da kwamitin harkokin ƙasashen waje sun nuna damuwa da wannan kuskuren, suna cewa mai neman zama jakada ya kamata ya nuna cikakken ƙwarewa.

Kara karanta wannan
Mutumin da Tinubu ya nada ya yi 'abin kunya' yayin tantance shi a Majalisar Dattawa
Majalisar dattawa na ci gaba da tantance mutane 65 da Shugaba Tinubu ya aiko domin mukaman jakadanci a fadin duniya bayan shekaru babu wakilci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

