Gwamna Radda Ya Yi Wa Malamai Babban Gata a Jihar Katsina
- Malaman makaranta a jihar za su dara a jihar Katsina bayan gwamnati ta fito da tsarin ba da alawus
- Gwamnatin jihar Katsina za ta fara biyan alawus ga malaman da aka tura zuwa yankunan karkara domin koyarwa
- Hakazalika, gwamnatin za ta samar da cibiyoyin horaswa domin karawa malamai kwarewa a fannin aikinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda ta amince da biyan alawus na N30,000 ga malaman da ake turawa kauyuka.
Gwamnatin ta amince da biyan alawus din ne domin kara musu kwarin gwiwa da magance matsalar karancin malamai a yankunan da ke da nisa.

Source: Facebook
Jaridar Leaderdership ta ce an yanke wannan shawara ne a taron majalisar zartarwar jihar karo na 18 da aka gudanar a ranar Laraba, 10 ga watan Disamban 2025 karkashin jagorancin Gwamna Dikko Radda.

Kara karanta wannan
Gwamna zai zuba jarin Naira biliyan 3.5 domin inganta makarantun musulmai a jiharsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Katsina za ta ba malamai alawus
Da yake hira da ’yan jarida a ranar Alhamis, kwamishinan ilmin firamare da sakandare, Yusuf Suleiman-Jibia, ya yi tsokaci kan shirin na ba da alawus.
Kwamishinan ya ce an tsara ba da tallafin ne duk karshen zangon karatu domin kara zaburar da malamai da kuma rage musu nauyin kuɗin da suke kashewa a yankunan karkara.
Yusuf Suleiman-Jibia ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kafa cibiyoyin horas da malamai a Katsina, Daura da Funtua, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Ya ce cibiyoyin za su inganta kwarewar malamai na firamare da sakandare ta hanyar horaswa ta musamman da za su rika samun daga kwararru na jami’o’i da tsofaffin malaman gwamnati.
A cewarsa, wannan mataki ya yi daidai da shawarwarin da aka bayar a wani taron da kungiyar Save the Children International (SCI) ta shirya a watan Satumba, tare da goyon bayan takawararta ta Education Cannot Wait.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Majalisa ta cimma matsaya kan bukatar Tinubu ta tura sojoji zuwa Benin
A taron, masu ruwa da tsaki sun jaddada bukatar karfafa malamai su karɓi aiki a yankuna marasa isassun malamai da kuma wuraren da ake fama da matsalar tsaro.
Meyasa za a ba malamai alawus?
Darakta a ma'aikatar, Hajiya Raliya Yusuf, ta ce manufar karin kuɗin ita ce a karfafawa malamai gwiwa su amince da a tura su ko da zuwa wuraren da suke da kalubalen tsaro kaɗan.

Source: Facebook
Ta bayyana cewa abin ya kai matakin damuwa ganin cewa yawancin malamai sun fi son su zauna a cikin birane, suna barin karkara babu malamai sosai.
A nata bangaren, manajan shirye-shirye ta SCI, Mrs. Atine Lewi, ta yaba da matakin, tana mai cewa:
“Mu da muke aiki domin inganta ilimi a Katsina, mun san irin tasirin wannan mataki. Wannan tallafi zai kara kwazon malamai kuma ya sa su ci gaba da zama a kauyuka inda ake bukatarsu fiye da ko’ina.”
Atine Lewi ta kara da cewa matakan da gwamnatin ta ɗauka suna nuna hangen nesa da niyyar aiwatar da sauye-sauye na gaskiya a bangaren ilmi.
Gwamna Radda ya yabi sulhu da 'yan bindiga

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yaba da suhu da 'yan bindiga.
Gwamna Radda ya yabawa al’ummomin da suke fama da matsalar tsaro saboda kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga a yankunansu.
Dikko Umaru Radda Gwamnan ya ce yarjejeniyar da al’ummomin suka kulla da ‘yan bindiga ta fara haifar da sakamako mai kyau.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng