Sanusi II Ya Yi Wa 'Yan Siyasa Tonon Silili, Ya Fadi Illar da Suka Yi Wa Najeriya

Sanusi II Ya Yi Wa 'Yan Siyasa Tonon Silili, Ya Fadi Illar da Suka Yi Wa Najeriya

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi tsokaci kan wasu daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya
  • Sanusi II ya bayyana cewa 'yan siyasa na taka rawar gani wajen hana Najeriya samun ci gaban da ya dace da ita
  • Hakazalika, ya bukaci matasa da su tashi tsaye su hada kai wajen samar da Najeriya wadda ta yi daidai da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan halin 'yan siyasa a Najeriya.

Muhammadu Sanusi II ya ce ’yan siyasar Najeriya suna hana ci gaban kasa da gangan, domin suna daukar mukaman gwamnati a matsayin daga su sai iyalansu.

Sanusi II ya yi magana kan halin 'yan siyasa
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II Hoto: @MSII_Dynasty
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta ce Sanusi II ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a bikin cika shekaru 15 na Enough is Enough (EiE) Nigeria a Legas, ranar Laraba, 10 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Sanata ya yi kumfar baki a majalisa bayan janye masa 'yan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sanusi II ya ce kan 'yan siyasa?

Sanusi II ya ce manyan ’yan siyasa sun kaurace wa damar habaka kasa saboda sun mayar da mukamin gwamnati na kansu, iyalansu da abokansu, ba domin kasa ko ’yan kasa ba.

“Mun yi wa kasarmu lahani sosai, watakila lokaci ne da ya dace mu tsaya haka nan. Kuma wannan shi ne abin da Omobola ke nufi game da damar da muke ta rasawa. Ba kawai rasa damarmaki ba, wani lokaci mu kan rasa su ne da gangan.”
“Wasu suna ganin mukamin gwamnati abu ne na kansu, iyalansu, ko na kusa da su ba na ‘yan kasa ba. Alhali kuwa mukamin gwamnati mallakar al’umma ne.”

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya zaburar da matasa

Sanusi II ya yi kira ga matasan Najeriya su ki karɓar Najeriya marar tsari da aka “kera” musu, su tashi tsaye su gina kasa mai cike da albarkatun da Allah ya yi mata.

Kara karanta wannan

Abin da Kiristoci suka fadawa dan majalisar Amurka da ya ziyarce su a Najeriya

Tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya (CBN) ya ce tsarin yanzu ya dogara ne kan rarrabuwar kabilu, rikice-rikicen addini, da gasa wajen tara mulki da abin duniya.

Ya ce dole ne matasa su haɗa kai su fitar da kyakkyawan tsari da hangen nesa na wata sabuwar Najeriya, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.

“Abu mafi muhimmanci shi ne mu tuna cewa kasar nan mallakinmu ce. Ba ta gwamnati bace, ba ta ’yan siyasa bace. Ta mu ce.”
“Duk inda muka samu kanmu, mu tuna muna rike da wani karamin ɓangare na Najeriya, kuma muna da alhakin bayar da gudummawarmu.”

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya koka kan halin 'yan siyasa
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II Hoto: @MSII_Dynasty
Source: Twitter

Sanusi II ya ba matasa shawara

Sanusi II ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su hada kai su gina wata dabarar siyasa mai ma’ana da hangen nesa kan irin Najeriya da muke so.

“Kuma dole ta zama Najeriya daban da wadda aka gina mana, wadda ta cika da rikicin kabila, rikicin addini, turka-turka ta neman gata, da gasa wajen tara karfin iko.”
“Dole mu kirkiri kasar da za ta kai ga matakin yin amfani da cikakken karfinta a cikin al’ummomin duniya.”

Kara karanta wannan

'Na gama yin shiru,' Matawalle ya tona wadanda ke daukar nauyin bata masa suna

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II bai je jana'izar Dahiru Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan rashin halartar jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sarkin ya bayyana cewa bai samu halartar jana'izar ba ne saboda lokacin ba ya cikin kasar nan, ya yi tafiya zuwa kasashen waje.

Sanusi II ya ce Sheikh Dahiru ya bar tarihin tausayi, zaman lafiya, koyi da kyawawan halaye da koyar da Musulunci cikin hikima da natsuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng