‘Game da Abacha ne’: Malami Ya Fadi Dalilin Tuhumar da EFCC Ke Yi Masa
- Tsohon ministan shari'a a Najeriya, Abubakar Malami ya fadi tambayoyi da hukumar EFCC ta yi masa bayan ziyartar ofishinsu
- Malami ya ce tambayar da EFCC ta yi masa ta tsaya ne kawai kan batun zargin dawo da kudin marigayi Sani Abacha
- Tsohon ministan ya bayyana cewa ba a taɓa tuhumarsa ko bincikensa a gida ko waje kan badakalar kudi ko asusun bankuna ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, SAN, ya bayyana tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa.
Malami ya ce tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa ta takaita ne kacokan kan bayyana batun zargin maimaita aikin dawo da kudaden Sani Abacha.

Source: Facebook
Malami ya fadi dalilin gayyatarsa da EFCC ta yi
A wata sanarwa daga ofishinsa, Malami ya karyata rahotannin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai game da zargin ta'addanci ba ne, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce babu wata hukuma ta tsaro ko leƙen asiri a Najeriya ko waje da ta taɓa zargensa ko bincikensa kan daukar nauyin ta’addanci ko mallakar asusun bankuna da yawa.
Tsohon ministan ya ce EFCC ta gayyace shi ne kawai domin ya fayyace batun dala miliyan 310 na kudin Abacha da aka dawo da su a zamanin gwamnatin Muhammadu Buhari.
Malami ya ce:
“Abin da EFCC ta tambaye ni shi kaɗai ya shafi zargin dawo da kudaden Abacha, Ba wani abu daban suka nemi bayani akai ba.”
Ya kara da cewa EFCC ta binciki batutuwan da suka shafi zargin cin mutunci da zargin badakalar kuɗi, amma bayan ya gabatar da cikakken bayani, hukumar ta ga babu wata hujja da za ta ci gaba da bincike.
Malami ya bayyana cewa bai yiwu a maimaita abin da bai kammala wanzuwa ba tun kafin 2016, yana mai tunawa da cewa lauyan Switzerland, Enrico Monfrini, ya rubuta wasiƙar neman a dawo da shi aikin ne a 2016 saboda aikin farko bai kai ƙarshe ba.

Source: Twitter
Yawan kudin Abacha da aka dawo da su
Ya ce gwamnatin Buhari ta ƙi biyan kuɗin da Monfrini ya nema, har zuwa dala miliyan biyar kafin aiki, sannan 40% na kudin da za a dawo, abin da ya sa aka zabi lauyoyi na cikin gida kan 5%, wanda ya ceto Najeriya biyan biliyoyin naira.
Malami ya kuma bayyana yadda kudaden Abacha daban-daban suka shiga Najeriya a lokuta daban-daban, Dala miliyan 322.5 daga Switzerland (2017–2018).
Ya ce duk ƙoƙarin haɗa waɗannan kudade ko nuna kamar an maimaita su bai wuce ɓata suna ba, kamar yadda Premium Times ta ce.
Malami ya kuma ce wani tsohon jami’in soja da ake zargin ya yi masa sharri kan daukar nauyin ta’addanci ma ya fito ya bayyana cewa ba shi ya yi wannan furuci ba.
Malami ya musanta zargin daukar auyin ta'addanci
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya yi tsokaci bayan an ambaci sunansa cikin mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci.
Abubakar Malami ya bayyana cewa ko sau daya ba a taba gayyatarsa a ciki ko wajen Najeriya kan batun da ya shafi daukar nauyin ta'addanci ba.
Malami wanda ya taba zama babban lauyan gwamnati ya bayyana manufar da mutanen da ke yada zargin daukar nauyin ta'addancin ke son cimmawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


