Mummunar Ambaliyar Ruwa Ta Afka wa Saudiyya, Jama'a Sun Rasu
- Ruwan sama mai tsanani ya yi sanadin mutuwar mutane a yankuna daban-daban na kasar Saudiyya tun farkon makon nan
- Hukumar kashe gobara ta kasar ta ce ta kubutar da mutane sama da 270 tare cewa fiye da 130 sun kaura daga gidajensu
- Hasashen yanayi ya nuna cewa ruwan sama, guguwar iska da hadari za su ci gaba a yawancin yankunan kasar Saudiyya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia – Aƙalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu bayan ruwan sama mai ɗimbin yawa ya sauka a yankuna da dama na Saudiyya tun ranar Lahadi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta kasar ta tabbatar.
Mummunan ruwan saman ya fi yin tasiri a yankunan Arewa maso Yammacin Saudiyya, kusa da iyakar ƙasar da Jordan.

Source: Getty Images
Rahoton Al-Jazeera ya ce mutane 10 sun mutu a birnin Tabuk, yayin da mutum ɗaya ya mutu a Madina da kuma wani a yankin Arewacin ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ruwan sama mai tsanani ya janyo ambaliya da kuma katse hanyoyi, sannan hukumomin ceto suka bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da kai agaji ga al’ummomin da lamarin ya shafa.
An ceto mutane 271 a ambaliyar Saudiyya
Hukumar kashe gobara ta bayyana cewa ta gano mutane 271 da ransu, waɗanda ambaliya ta rutsa da su a yankuna daban-daban na masarautar Saudiyya tun daga ranar Lahadi zuwa yau.
Rahoton Gurlf News ya bayyana cewa a cikin yankin Tabuk kaɗai an karbi mutane 137 bayan gidajensu sun cika da ruwa makil.
Kafofin yaɗa labaran Saudiyya sun tabbatar da cewa duk da ruwan bai yi tsanani a Riyadh da Jeddah ba, ya haddasa katsewar lantarki a wasu unguwanni.
Saudiyya na tantance barnar ambaliyar
Rahotanni sun nuna cewa an kafa kwamitoci daban-daban domin tantance adadin barnar da ambaliyar ta yi, musamman a yankunan da ruwan sama mai karfi ya fi shafa.

Source: Getty Images
Masu lura da yanayi sun ce irin barnar da aka samu na nuna bukatar ma’aikatu da hukumomin tsaro su kara sa ido, domin an yi hasashen karin ruwan sama a nan gaba.
Hasashen yanayi a kasar Saudi Arabiya
Cibiyar kula da yanayi ta NCM ta yi hasashen cewa za a ci gaba da samun ruwan sama mai karfi, hadari, iska mai tsanani da kuma yiwuwar ambaliya a yankunan Makkah, Madina, Qassim, Riyadh, Yankin Gabas da Arewacin kasar.
Bugu da ƙari, ana sa ran ruwan sama matsakaici a Hail, Tabuk da Al Jouf, tare da hazo a wasu lokuta a tsaunukan Kudu maso Yamma.
NCM ta ce iska a Tekun Ja za ta rika kadawa daga Arewa maso Yamma zuwa Arewa, sannan daga Kudu maso Gabas zuwa Kudu yayin da ake hasashen guguwa a yankin Bab Al Mandeb.
Mutane 45 sun rasu a hadarin Saudiyya
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta tabbatar da rasuwar wasu mutane 45 a hadarin tankar mai.
Hukumomi sun bayyana cewa mutanen sun fito ne daga kasar Indiya zuwa Saudiyya domin gabatar da ibadar Umara.
Shugabannin Indiya da suka hada da Firaministan kasar sun bayyana cewa sun yi magana da Saudiyya kan mummunan hadarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


