Kisan Zaria: Sheikh Zakzaky Ya Fadi Abin da Ya Rage tsakaninsa da Buhari duk da Ya Rasu

Kisan Zaria: Sheikh Zakzaky Ya Fadi Abin da Ya Rage tsakaninsa da Buhari duk da Ya Rasu

  • Shugaban kungiyar 'yan shi'a ta Najeriya (IMN), Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewa za su hadu da mrigayi Buhari a gaban Allah
  • Zakzaky ya fadi haka ne yayin da yake jawabin ga manema labarai bayan cika shekaru 10 da arangamar sojoji da yan shi'a a Zaria
  • Malamin addinin musulunci ya koka kan yadda har yau gwamnati ta gaza daukar laifin abin da ya faru ballantana ta tausaya wa iyalan wadanda aka kashe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Kungiyar 'Yan Shi'a ta Najeriya (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya yi magana kan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Sheikh Zakzaky ya kuma koka kan yadda har yanzu gwamnati ta gaza fitar da cikakken rahoton binciken da aka yi bayan arangamar sojoji da 'yan shi'a a Zaria, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa dan sandan Najeriya hukuncin kisa, za a rataye shi har lahira

Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Shugaban kungiyar 'yan shi'a ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky Hoto: Sheikh Ibrahim Zakzaky
Source: Facebook

Malamin akidar shi'a ya ce shi da Buhari za su tsaya a gaban Allah domin ya yi hisabi kan abin da ya faru a rikicin Zaria shekaru goma da suka gabata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya faru da 'yan shi'a a Zaria

Rikicin ya faru ne lokacin mulkin Buhari, bayan hatsaniya da ta samo asali daga toshe hanyar da yan Shi'a suka yi wa tawagar tsohon Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, a Zaria.

Abin da ya fara da ƙaramin sabani ya rikide zuwa luguden wuta, inda sojoji suka bude wa mabiyan Sheikh Zakzaky wuta.

Rahotannin kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ce sama da mutane 300 aka kashe aka binne su a boye, yayin da kwamitin bincike na gwamnati ya bayyana cewa fiye da 1,000 ne suka rasa rayukansu.

Gwamnati ta kama tare da tsare Zakzaky da matarsa, Zeenat, na tsawon shekaru kafin kotu ta wanke su a 2021, cewar rahoton DW Hausa.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 4, an samu labarin rasuwar tsohon 'dan Majalisar Tarayya a Najeriya

Zakzaky koka kan rashin daukar mataki

A taron manema labarai da ya kira domin cika shekaru 10 da faruwar lamarin, Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da ma gwamnati mai ci yanzu, da kin fitar da rahoton bincike na gaskiya, ko tausayawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Ya ce:

"Ba abin da aka yi tun tuni, gwamnati ba ta yarda ma wani abu ya faru ba, gani suke karya ne, duk da kwamitin bincike ya hada rahoto ya mika masu ranar 7 ga watan Satumba, 2016 amma babu abin da aka yi.
Zakzaky da Buhari.
Shugaban kungiyar IMN ta mabiya akidar shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky da marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Sheikh Ibrahim Zakzaky, Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Abin da Sheikh Zakzaky ya fada kan Buhari

Da aka tambaye shi ko ya yafe wa Buhari, sai ya ce:

“Batun Buhari, abu ne mai sauki, ya riga ya mutu. Zamu hadu a ranar Lahira domin bamu yafe abin da aka mana ba.
"Na gaya wa ministansa tun lokacin da aka harbe ni ina cikin jini, ku gaishe shi. Zamu hadu a lahira, dan haka batun Buhari ya kare.”

Kara karanta wannan

Ta fasu: Muhuyi Magaji ya fadi dalilin da ya sa 'yan sanda suka cafke shi

Shehin malamin ya ce duk kokarin da aka yi don “murkushe” IMN bai yi nasara ba, domin maimakon haka ya ƙara bunkasa ƙarfin kungiyar a duniya.

Zakzaky ya yi alhinin rasuwar Dahiru Bauchi

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya bi sahun masu mika sakon ta'aziyyarsu kan rasuwar Dahiru Bauchi.

Sheikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana bakin cikinsa matuka kan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi , wanda ya yi bankwana da duniya a ranar Alhamis.

Malamin ya roki Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya yi masa rahama, kuma ya ba shi matsayi mai girma a gidan Aljannah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262