Mutumin da Tinubu Ya Nada Ya Yi 'Abin Kunya' yayin Tantance Shi a Majalisar Dattawa
- Daya daga cikin wadanda Shugaba Tinubu ya nada a matsayin jakadu ya gaza ambatar sunayen sanatoci uku a gaban Majalisar Dattawa
- Hakan dai ya faru ne yayin da kwamitin kula da harkokin kasashen waje ya fara aikin tantance sababbin jakadu a ranar Laraba
- Mambobin kwamitin sun nuna damuwa kan abin da sabon jakadan ya yi, inda suka bayyana shi da abin kunya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kwamitin kula da harkokin kasashen ketare na Majalisar Dattawa ya fara aikin tantance sababbin jakadun Najeriya da Shugaba Bola Tinubu ya nada.
Kwamitin, wanda Majalisar Dattawa ta dora wa alhakin tantance sababbin jakadun ya fara aikinsa, amma ya gamu da abin da bai yi tsammani ba yayin tantance mutum daya daga ciki yau Laraba.

Source: Facebook
Abin da ya faru a zaman tantance jakadu
Daily Trust ta rahoto cewa mambobin kwamitin sun sha mamaki a lokacin da suka fara tantance, Emmanuel Adeyemi, wanda Tinubu ke son ya zama jakada daga jihar Ekiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adeyemi, ya kasa ambaton sunan ɗaya daga cikin sanatocin jiharsa ta Ekiti guda uku, lamarin da ya ba mambobin kwamitin mamaki da takaici.
Emmanuel Adeyemi, wanda shi ne Mataimakin Darektan Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje, ya sha yabo a farko fara tantance saboda ƙwarewarsa daga aikin jakadanci a Hong Kong da Faransa har zuwa samun digirin PhD.
Amma lamarin ya canza zani ne lokacin da ya yi kokarin mika gaisuwa ga sanatocin jiharsa ta Ekiti, inda ya ambaci sunayen mutum biyu daga ciki, amma dayan ya makale.
Adeyemi ya ambaci sunan Sanata Opeyemi Bamidele, shugaban masu rinjaye na Majalisar dattawa da Sanata Yemi Adaramodu, mai wakiltar Ekiti ta Arewa.
Amma ya kasa tuna sunan na uku Sanata Cyril Fasuyi (Ekiti ta Arewa). Wasu mambobin kwamitin sun lura da wani daga tawagarsa yana ƙoƙarin duba sunan a Google.
Sanatoci sun nuna rashin jin daɗi
Sanata Asuquo Ekpenyong, wanda ke cikin kwamitin da ke tantance jakadun ya nuna damuwa, yana mai cewa wannan kuskure na nuni da cewa wasu masu neman mukaman kasa ba su shirya ba.
Sanata Adams Oshiomhole da Sanata Seriake Dickson ma sun goyi bayan wannan magana ta abokin aikinsu.
Mambobin kwamitin sun bayyana lamarin a matsayin abin kunya kuma abin da ba za a iya amincewa da shi ba.

Source: Facebook
Sababbin jakadun da aka tantance
Sai dai Sanata Yunus Akintunde, wanda ya wakilci Sanata Bamidele, ya roki a yi wa Adeyemi afuwa, kamar yadda jaridar Leadership ta kawo.
Adeyemi na cikin jerin mutane uku daga Ekiti da aka tura domin zama jakadu tare da Erelu Angela Adebayo da Olumilua Oluwayemika.
Kwamitin ya kuma tantance Ahmed Sulu Gambari, Maimuna Besto, Monica Enebechi, Ahmed Monguno, Kingsley Onaga, Magaji Umar da Aminu Nasir.
Ndume ya soki nadin sababbin jakadu
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya soki jerin sababbin jakadun Najeriya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura Majalisar Dattawa domin tantancewa.
Ndume ya bukaci Tinubu ya janye jerin sunayen jakadu da ya tura majalisar dattawa saboda ba su mutunta tsarin doka da tanadin kundin tsarin mulki ba.

Kara karanta wannan
Sanata Ndume na neman dawo da hannun agogo baya game da jakadun da Tinubu ya nada
Ya koka kan yadda wasu jihohi suka samu har guda uku ko huɗu, wasu kuwa ba su samu ko mutum ɗaya ba, ciki har da Jihar Gombe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

