Bayan Korafe Korafe, Tinubu Ya Bada Sabon Umarni kan Janye 'Yan Sanda daga Gadin Manya

Bayan Korafe Korafe, Tinubu Ya Bada Sabon Umarni kan Janye 'Yan Sanda daga Gadin Manya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake tabo batun umarnin da ya bada na janye jami'an 'yan sandan Najeriya daga gadin manya
  • Mai girma Bola Tinubu ya nuna ba da wasa ya zo ba kan matakin da ya dauka na ganin cewa 'yan sanda sun koma aikin da ya wajaba a kansu
  • Shugaban kasar ya sake jaddada umarninsa na janye 'yan sandan saboda abin da ya kira ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabo batun umarnin da ya ba da na janye jami'an 'yan sanda daga gadin manya.

Shugaba Tinubu ya sake jaddada umarninsa na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane domin mayar da su kan aikin tsaro na ainihi.

Tinubu ya sake umartar a janye 'yan sanda daga gadin manya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya sake umartar janye 'yan sanda

Kara karanta wannan

Sanata ya yi kumfar baki a majalisa bayan janye masa 'yan sanda

Jaridar The Punch ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne daƙiƙu kaɗan kafin ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta kasa (FEC) a fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Laraba.

“Na yi amanna da abin da na faɗa. A aiwatar da shi. Idan kuma akwai wata buƙata saboda nau’in aikinka, ka tuntuɓi IGP, ka samu izini na.”

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaban kasar ya nuna muhimmancin gaggawar da ake bukata wajen bin umarnin, yana nuna alamun gajiya da jinkirin aiwatarwa, jaridar Leadership ta kawo labarin.

Tinubu ya samo mafita ga manyan mutane

Ya umurci Ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi aiki tare da Sufeto Janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun, da Hukumar Sibil Difens domin gaggauta maye gurbin jami’an tsaron da aka janye, domin kada a bar mutane a ba tare da kariya ba.

“Ministan harkokin cikin gida ya tuntuɓi IGP da Sibil Difens don su maye gurbin jami’an ’yan sandan da aka janye daga ayyuka na musamman. Kada a bar mutane ba kariya.”

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya kuma umarci mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin taro (NSA), Nuhu Ribadu, da DSS su tabbatar da cewa an aiwatar da dokar yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi maraba da ceto daliban Neja, ya ba jami'an tsaro sabon umarni

“NSA da DSS za su samar da karin bayanai, su kafa kwamiti, su sake duba tsarin.”

- Shugaba Bola Tinubu

Me yasa Tinubu ya bada umarnin?

Shugaba Tinubu ya danganta wannan mataki da karuwar hare-haren garkuwa da mutane a fadin kasar.

Shugaba Tinubu ya umarci a janye 'yan sanda daga gadin manya
Mai girma Bola Ahmed Tinubu na jawabi a wajen taro Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook
“Muna fuskantar kalubalen garkuwa da mutane. Muna buƙatar dukkan jami’an tsaro da muke da su su yi aiki yadda ya kamata.”

- Shugaba Bola Tinubu

Ya kara da cewa duk da cewa akwai wasu jami’an gwamnati da suke cikin haɗari, jami’an Sibil Difens za su iya ci gaba da kare su idan akwai bukata.

“Na san wasu mutane na cikin haɗari, kuma zan yi la’akari da samar musu da kariya ta musamman. Sibile Difens suna da makamai."

- Shugaba Bola Tinubu

Sanata ya koka kan janye masa dan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya korafi a gaban majalisar dattawa.

Sanata Abdu Ningi na jam'iyyar PDP ya nuna damuwa kan janye masa jami'in dan sanda guda daya tilo da yake ba shi kariya.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 sun dura fadar Aso Rock, sun shiga ganawa da Shugaba Tinubu

Abdul Ningi ya yi korafin cewa bai kamata a janyewa sanatoci jami'an tsaro ba sannan a bar wasu shafaffu da mai suna yawo da 'yan sanda ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng