Sanata Ya Yi Kumfar Baki a Majalisa bayan Janye Masa 'Yan Sanda
- A kwanakin baya Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin janye jami'an 'yan sanda daga gadin manya
- Sanata Abdul Ningi ya yi korafi a gaban majalisar dattawa bayan an janye masa dan sandan da yake ba shi kariya
- Abdul Ningi ya koka da cewa yayin da aka janyewa sanatoci 'yan sanda, an bar wasu manya a gwamnati tare da jami'an tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya ɗaga batun gaggawa a zauren majalisar dattawa.
Da ya mike domin ya yi magana, Sanata Abdul Ningi ya yi korafin cewa an janye masa ɗan sanda guda daya tilo da ke tare da shi.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce Sanatan ya yi korafin ne yayin zaman majalisar dattawa na ranar Laraba, 10 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane korafi Sanata Abdul Ningi ya yi?
Sanata Ningi ya dage cewa ya zama tilas a aiwatar da umarnin shugaban kasa na janye 'yan sanda ga kowa, ba wai a takurawa ’yan majalisa kaɗai ba, jaridar The Punch ta dauko labarin.
Ya ce duk da cewa an cire masa ɗan sanda guda ɗaya da yake da shi, akwai sauran nau’o’in mutane da dama ciki har da ministoci, gwamnonin jihohi, ’yan kasuwa, har ma da mawaƙa da ke ta amfani da jami’an tsaro ba tare da wata matsala ba.
“Ya kamata a yi adalci. Mu gani daga ofishin shugaban kasa, zuwa mataimakinsa, zuwa shugaban majalisar dattawa, shugaban majalisar wakilai da ministoci."
"Na ga ministoci biyu jiya da rakiyar jami’an tsaro masu yawa. Na ga ’yan kasuwa, 'yan China da sauran kamfanoni, suna da jami'an tsaro"
"Na ga yara maza da mata na manyan ’yan siyasa da ma mawakan da ke yawo da jami’an tsaro."
“Amma Sanatan Tarayyar Najeriya wanda ya shafe dogon lokaci a nan, yana da guda ɗaya tilo, shi ma an zo ana janyewa. Hakan ba ya faruwa a kowace dimokuraɗiyya.”
- Sanata Abdul Ningi
Sanatan ya bukaci a yi adalci
Ya bayyana aiwatar da dokar kan ’yan majalisa kaɗai a matsayin babban rashin adalci, yana rokon shugaban majalisar dattawa da ya umurci kwamitin harkokin ’yan sanda ya yi bincike.
“Idan dai za a yi, a yi wa kowa. Ni zan iya kare kaina, amma kada na ga gwamnoni, ministoci, da ’yan kasuwa suna samun rakiya ta jami’an tsaro yayin da mu kuma ake takura mana.”
- Sanata Abdul Ningi

Source: Facebook
Majalisar dattawa ta dauki mataki
A yayin da yake jagorantar zaman, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tabbatar wa Ningi cewa shugabancin majalisar ya riga ya ɗauki mataki kan lamarin.
"Ina sanar da kai cewa shugabancin majalisa ya tattauna kan batun jiya, mun kuma ɗauki matakin da ya dace. Muna jiran bayani kan janye 'yan sanda da aka yi wa Sanatoci."
- Barau Jibrin
Majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince da sabuwar bukatar da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar mata kan yunkurin juyin mulkin da aka a yi a Jamhuriyar Benin.
Majalisar dattawan ta amince shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura dakarun sojoji zuwa Benin bayan an yi yunkurin kifar da gwamnati.
Dukkan Sanatocin da suka halarci zaman majalisar sun kada kuri’a cikin goyon baya, wanda hakan ya bada cikakken izini na doka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


