An Ƙara Yawan Ƴan Sanda a Adamawa don Hana Faɗan Kabilan

An Ƙara Yawan Ƴan Sanda a Adamawa don Hana Faɗan Kabilan

  • Rundunar ‘yan sandan Adamawa ta tura ƙarin jami’ai bayan gwamnati ta kafa takunkumin fita na sa’o’i 24 a Lamurde
  • An umarci mazauna yankunan da su zauna a gidajensu don kauce wa ƙarin rikici da tabarbarewar tsaro da ya addabi yankin
  • Harin da ake zargin mayakan ƙabilu daga Gombe ne suka kai ya yi sanadin mutuwa da lalata kauyuka da dama duk da batun sulhu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa – Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ta sanar da tura ƙarin jami’ai da kayan aiki zuwa Karamar Hukumar Lamurde.

Lamarin na zuwa ne bayan da gwamnatin jiha ta ayyana takunkumin fita na sa’o’i 24 saboda sake barkewar rikicin kabilanci a yankin.

Yan sanda sun fara ɗaukar matakin dakile dawowar rashin tsaro
Wasu daga cikin jami'an yan sandan Najeriya Hoto: Nigerian Police Force
Source: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa Kakakin rundunar, Suleiman Nguroje, ya ce an bukaci al’umma su bi umarnin takunkumin su zauna a gidajensu.

Kara karanta wannan

Jama'a sun fito titunan Sakkwato murnar hallaka kasurgumin ɗan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta sa dokar hana fita a Adamawa

Jaridar Punch ta wallafa cewa rundunar ƴan sandan Adamawa ta aika ƙarin mutanen domin tabbatar da zaman lafiya da hana ɓarkewar sabuwar tarzoma.

Suleiman Nguroje ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Dankombo Morris, ya bayar da umarnin ƙara tsaurara matakan sa ido a dukkanin yankunan da ake rikicin.

Jami’an tsaro, a cewarsa, suna kewaye domin tabbatar da an kiyaye doka, a maido da natsuwa, tare da kare rayuka da dukiyoyi ta duk wata hanya da doka ta tanada.

Yan sanda suna aikin tsare rayuka a Adamawa

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kwantar da tarzoma da wanzarda zaman lafiya.

Ta gargadi mazauna yankin su guji duk wani abu da ka iya tayar da hankali ko haifar da sabon tashin hankali a wannan lokaci mai sarkakiya.

A sanarwar, rundunar ta ce ba za ta lamunci bata-gari ko wasu da ke ƙoƙarin haifar da tarzoma su yi abin da suka ga dama ba.

Kara karanta wannan

Rawar da Faransa ta taka wajen tarwatsa masu yunkurin juyin mulki a Benin

An shawarci jama'a su bi dokar hana zirga-zirga
Taswirar jihar Adamawa, inda ake samun matsalar kabilanci Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta ƙara da cewa jami’an da aka tura za su yi aikinsu cikin ƙwarewa ba tare da amfani da karfi fiye da kima ko abin da zai janyo rasa rayuka ba yayin aiwatar da takunkumin fita.

Harin da ya faru ranar Lahadi ya tada hankulan jama’a a fadin jihar, bayan da rahotanni suka nuna cewa wasu mayakan ƙabilu kai hare-hare a kauyukan Bachama na Lamurde.

Gwamnatin Adamawa ta sa dokar hana yawo

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri, ya ayyana dokar ta-ɓaci na tsawon awanni 24 a Karamar Hukumar Lamurde.

Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar ƙarin tashin hankali a tsakanin al’ummomin da abin ya shafa, kuma ya jawo asarar rayuka.

Sanarwar dokar ta-ɓacin ta fito ne daga sakataren yaɗa labarai na mataimakin gwamna, Hussaini Hammangabdo, wanda ya sanya wa takardar hannu a ranar 8 ga Disamba, 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng