Yadda Asirin Mai Garkuwa da Mutane Ya Tonu a wajen Cire Kudin Fansa a POS
- ’Yan sanda sun cafke wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane yayin da yake ƙoƙarin cire kudin fansa a wani shagon POS
- A cewar rundunar ’yan sanda, mutumin ya yi wa matar aure barazana da bindiga sannan ya tilasta ta kira mijinta domin neman kudi
- Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin gano ko akwai wasu da ke taimaka masa a aikata laifuffukan garkuwa da mutane a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo – Rundunar ’yan sandan jihar Ondo ta kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane, Godspower Cletus, bayan da aka tarar da shi yana ƙoƙarin cire N1m da ya karɓa a matsayin kudin fansa.
Rahotanni sun ce an kama shi ne a wani shagon POS bayan ya yi wa wata mata barazana tare da karɓe wayarta da katin bankinta na ATM.

Source: Facebook
Rahoton Vanguard ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kutsa cikin gidan Farimoyo Endurance da ke unguwar Odudu a Akure, inda ya yi mata barazana da bindiga kafin ya tilasta ta kira mijinta domin neman kudin fansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mijin nata ya tura N1m zuwa asusun Opay na matarsa bayan barazanar da aka yi mata, lamarin da ya bai wa wanda ake zargin damar tserewa da tunanin ya ci nasara.
Yadda aka gano mai garkuwa da mutane
Bayan faruwar lamarin, rundunar ’yan sanda ta tura jami’anta na sashen kula da garkuwa da mutane domin gudanar da bincike.
Rahotanni sun nuna cewa ta hanyar tattara bayanan leƙen asiri, jami’an sun bi sawun wanda ake zargin har zuwa shagon POS da yake son cire kudin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Ayanlade Olayinka, ya bayyana cewa wannan aiki na nuna ƙwarewar rundunar wajen kai farmaki ga masu aikata laifi kafin su sami damar ɓuya.
Olayinka ya ce bayan kama shi, mutumin ya amsa laifinsa ba tare da tilastawa ba, kuma bincike ya fara domin gano ko yana da abokan aikata irin waɗannan laifuffuka a jihar.
An jinjina wa 'yan sanda a Ondo
Mai magana da yawun rundunar ya jinjina wa jami’an saboda irin saurin da suka yi wajen gano wanda ake zargi da satar mutane.
Ya ce wannan nasara na nuna irin ƙoƙari da ingancin dabarun aiki da rundunar take aiwatarwa domin rage laifuffuka a jihar.
Tribune ta rahoto kakakin rundunar ya ce:
“Hanzarin da jami’an suka nuna ya tabbatar da cewa rundunar ta ƙara ƙwarewa wajen gano masu aikata laifi tare da dakile su tun kafin su tsere.”
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Adebowale Lawal, ya bayyana cewa nasarar ta sake tabbatar da karfin rundunar wajen fatattakar masu aikata laifuffuka musamman a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

Source: Original
A cikin sanarwar, rundunar ta ja hankalin jama’a su kasance cikin shiri da lura musamman a lokacin bukukuwa, tare da yin hanzari wajen kai rahoton duk wani motsi ko ayyukan da suka zama abin zargi.
An yi rikicin kabilanci a jihar Taraba
A wani labarin, kun ji cewa an samu wani kazamin rikicin kabilanci da ya jawo asarar rayuka a wasu yankuna na jihar Taraba.
Bayan mutuwar wasu mata a rikicin, rahotanni sun nuna cewa an zargi wasu dakarun Najeriya da cewa su suka harbe su.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojojin Najeriya ta yi bayani dalla-dalla game da abin da ya faru a lokacin rikicin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


