Tsaro: Malaman Musulunci, Kirista Sun Fadawa Tinubu Gaskiya, Sun Hango Barazana
- Manyan shugabannin addinai da na gargajiya sun ba Bola Ahmed Tinubu shawarwari kan tabarbarewar tsaro a Najeriya
- Taron ya jaddada cewa babu addinin da ya halatta kashe-kashe, suna kira ga limamai su hade wuri guda wajen kare mutunci da rayuka
- An amince a kafa kwamiti na hadin guiwa domin inganta sulhu, karfafa raunin zukata da zaman lafiya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — Manyan shugabannin addinai na Kirista da Musulunci, da sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban, sun aika sako kai tsaye ga Bola Tinubu.
Shugabanni addinan sun nuna cewa rikice-rikicen tsaro da ke ƙara ta’azzara a kasar sun dawo gabansa baki daya.

Source: Facebook
An gargadi Bola Tinubu kan rashin tsaro
Rahoton Vanguard ya ce shugabannin addinan sun bayyana matsalar a matsayin ta gaggawa da ta shafi kasa da ke bukatar tsauraran matakai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin sun kuma gargadi Majalisar Dokoki cewa ba su da hurumin yin doka idan al’ummomin da suka zabe su suna fama da hare-hare da kashe-kashe ba tare da kariya ba.
Wannan matsaya ta fito ne a wani Babban Taron Musayar Ra’ayin Addinai kan ‘Yancin Addini da Tsaron Dan Adam da aka gudanar a Abuja.
Wadanda suka halarci taron a Abuja
Taron ya hada manyan fitattun jiga-jigan addinai kamar babban Fasto John Onaiyekan da Sheikh Nurudeen Lemu da Rabaran Stephen Panya Baba.
Sai kuma Sheikh Nuru Khalid, Fasto Sunday Onuoha, Fasto Canice Chinyeaka Enyiaka, Sarkin Bangudu, da Sarkin Doma, da sauransu.
Duk da cewa sun yarda matsalolin tsaro sun dade kafin gwamnatin Tinubu, sun jaddada cewa yanzu shi ne ke da cikakkiyar dama da nauyin jagorantar kasar zuwa zaman lafiya.
Masu jawabi da dama sun nuna cewa babu wani addini da ya amince da barna ko cutar da marasa laifi, suna kira ga limamai su yi hadin kai domin dakile yadda ake amfani da addini wajen aikata barna.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu
Rabaran John Hayab ya ce taron yana da nufin karfafa hadin kai da tsayuwar daka wajen kare ’yancin rayuwa da addini a kasar, cewar FRCN HQ.

Source: Facebook
'Babu addinin da ya halatta kashe-kashe
A nasa jawabin, Fasto Canice Chinyeaka Enyiaka ya ce tashin-tashinar da ake fuskanta ba wai na siyasa kadai ba ne har ma da na rayuwa.
Ya tunatar da mahalarta cewa koyarwar addinai duk suna kare mutunci da darajar rayuwa.
A bangaren siyasa, sanarwar ta ce:
“Matsalolin Najeriya sun gabaci Shugaba Tinubu, amma shi ke da nauyin magance su yanzu. Duk wani cigaba zai zama babu amfani idan ba a magance tsaro ba.”
Fasto Sunday Onuoha ya shawarci gwamnati ta nemi taimakon kasashen waje idan ya zama dole, amma ta kare ikon Najeriya.
Ya ce:
“Ina rokon gwamnati, kamar yadda muke karbar lamuni daga kasashen waje, za mu iya neman taimako, amma a kiyaye mutuncin kasar.”
Gwamnatin Tinubu za ta taimaka wa Benin da tsaro
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu zai taimakawa Jamhuriyar Benin da karin dakarun sojoji bayan ta shiga cikin barazanar kifar da gwamnati.
Tun a farkon makon nan labari ya zo cewa Tinubu ya samu amincewar Majalisar Dattawa ta amince domin daukar mataki mai tsauri a kasar.
Hakan ya biyo bayan yunkurin juyin mulki da sojoji suka yi a kasar wanda bai yi nasara ba a ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

