Juyin Mulki: Majalisa Ta Cimma Matsaya kan Bukatar Tinubu Ta Tura Sojoji zuwa Benin

Juyin Mulki: Majalisa Ta Cimma Matsaya kan Bukatar Tinubu Ta Tura Sojoji zuwa Benin

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da wasika zuwa ga majalisar dattawa inda ya bukaci ta amince ya tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin
  • Mai girma Bola Tinubu ya aika da bukatar ne domin dawo da zaman lafiya a kasar mai makwabtaka da Najeriya biyo bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi
  • Majalisar dattawa ta yi zama a ranar Talata, inda ta sahalewa shugaban kasar ya tura dakarun sojojin Najeriya zuwa Benin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na tura dakarun Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin.

Majalisar ta amince a tura dakarun ne domin tallafa wa kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a kasar a karshen mako.

Majalisa ta amince Tinubu ya tura sojoji zuwa Benin
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da sojojin Najeriya Hoto: @SenateNGR, @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da haka a ranar Talata yayin zaman majalisar na ranar Talata, 9 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: 'Matakin da Tinubu ya dauka a Benin ya dakile barazanar da ta tunkaro Najeriya'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta amince da bukatar Tinubu

Amincewar na zuwa ne bayan ‘yan majalisar sun tattauna bukatar bisa tanadin sashe na 5, bangare na II na kundin tsarin mulki, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.

Dukkan Sanatocin da suka halarta sun kada kuri’a cikin goyon baya, wanda hakan ya bada cikakken izini na doka ga wannan matakin tsaro na yankin.

Akpabio ya bayyana matakin a matsayin “hanya madaidaiciya,” yana mai jaddada cewa duk wani tashin hankali a kasa makwabciya barazana ce ga dukkan yankin.

Shugaban majalisar dattawan ya ce duk abin da ya shafi dan uwanka to tabbas ya shafe ka, yana mai cewa dole ne Najeriya ta tallafa wa kasashen ECOWAS wadanda suke abokan hulɗarta.

A halin yanzu za a tura wasikar amincewar Majalisar Dattawa zuwa ga Shugaba Tinubu.

Tinubu ya bukaci tura sojoji zuwa Benin

Tun da farko, Shugaba Tinubu ya rubuta wa majalisar dattawa wasika yana neman izinin tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu zai tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin

Shugaba Tinubu bayyana cewa Najeriya na da alhakin tarihi na taimaka wa kasar bisa yarjejeniyoyin tsaro ta ECOWAS.

A cewar Shugaban, halin da ake ciki na bukatar daukar matakin gaggawa daga waje domin dawo da zaman lafiya kuma a hana kara tabarbarewar lamarin.

Tinubu ya so tura sojoji zuwa Benin
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

An yi yunƙurin juyin mulkin ne a ranar Lahadi, lokacin da wasu dakarun sojoji suka sanar da cewa sun hambarar da Shugaba Patrice Talon.

Amma rundunar sojojin kasar ta fatattaki masu yunkurin juyin mulkin, ta kuma dawo da iko.

Bayan faruwar lamarin, ECOWAS ta bayyana cewa za ta tura tawagar dakarun sojoji domin tallafawa da tabbatar da tsaro a yankin.

Sanata Barau ya yabawa Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yabawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Barau ya yabawa Shugaba Tinubu dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin matsayin muhimmin mataki na kare dImokiradiyya a yammacin Afrika.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce Shugaba Tinubu ya yi abin da ya dace da ya amsa rokon neman agajin Jamhiruyyar Benin a cikin gaggawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng