Juyin Mulki: Tinubu Zai Tura Sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin
- Shugaba Bola Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince domin daukar mataki mai tsauri a Jamhuriyar Benin
- Hakan ya biyo bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a kasar wanda bai yi nasara ba a ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025
- Tinubu ya ce Benin ta nemi tallafin jiragen yaki na Najeriya, domin dakile barazanar yan tawaye da ke neman rusa dimokuraɗiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya roƙi majalisar dattawa ta amince da tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin.
Hakan na daga cikin kokarin wanzar da zaman lafiya, bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi wa Shugaba Patrice Talon.

Source: Twitter
Rahoton Punch ya ce Tinubu ya rubuta wasika ga majalisar dattawa wanda shugabanta, Godswill Akpabio ya karanto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka yunkurin juyin mulki a Benin
Wannan bukata ta fito ne kwana biyu bayan wasu sojoji yan tawaye sun mamaye gidan talabijin a birnin Cotonou, babban cibiyar kasuwanci ta Benin, kafin daga bisani hukumomi su fatattake su.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025 da muke ciki wanda ya tayar da hankulan kasashe makwabta.
Hankula sun tashi a kasar bayan yunkurin sojoji da kuma ikirarin hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon wanda ya jawo hankalin kasashen Afirka.
Martanin gwamnatin Benin kan juyin mulki
Sai dai, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa masu yunkurin juyin mulkin ba su karbe iko ba a kasar da ke yankin Afrika ta Yamma.
Kasar Benin dai na da tarihin juyin mulki da yunkurin kifar da gwamnatoci da dama tun shekaru da dama da suka gabata.

Source: Facebook
Benin: Wasikar Bola Tinubu zuwa ga majalisa
A cikin wasiƙar, Tinubu ya nemi sahalewar majalisar kan tura dakarun Najeriya, tare da bayyana cewa Benin ta roƙi taimakon gaggawa, musamman na jirgin sama na soji, domin kiyaye tsarin mulki da daidaita al’amuran tsaro.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu
Ya ce:
“Gwamnatin Jamhuriyar Benin na fuskantar yunƙurin kifar da gwamnati ta hanyar da ba ta dace ba, lamarin da ke barazana ga dimokuraɗiyya. Sun bukaci taimakon waje cikin gaggawa.”
Tinubu ya kuma tuna wa majalisa cewa akwai zumunci mai ƙarfi tsakanin Najeriya da Benin, tare da ƙa’idojin tsaron haɗin gwiwa da ECOWAS ke bin su wajen kare tsarin dimokuraɗiyya a yankin.
Ya roƙi majalisar ta amince da bukatar ba tare da bata lokaci ba, tare da nuna godiyarsa ga dattawan majalisar saboda goyon bayan da suke baiwa ƙasar, cewar TheCable.
Daga baya, Channels TV ta ruwaito cewa Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya sanar da haka a zaman majalisa na ranar Talata 9 ga watan Disambar 2025, bayan 'yan majalisar sun tattauna.
Sanatocin sun kada kuri’ar amincewa gaba ɗaya, wanda ya bai wa Gwamnatin Tarayya sahalewar doka don gudanar da wannan aikin tsaro a yankin.
Benin: Kokarin Tinubu yayin yunkurin juyin mulki
A baya, kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da yunurin juyin mulki da sojoji suka yi a Benin, tana mai yabon matakan gaggawa aka dauka.
Wasu matakai da Najeriya ta dauka sun hada da tura jiragen yaki zuwa sararin samaniyar Benin don dakile duk wata barazana ga kasar.
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da aiki tare da Benin da sauran kasashen ECOWAS domin hana sake bullar irin wadannan rikice-rikice.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

