"Kar Ku Zama 'Yan Kallo": Atiku Ya Yi Muhimmiyar Nasiha ga Matasan Najeriya

"Kar Ku Zama 'Yan Kallo": Atiku Ya Yi Muhimmiyar Nasiha ga Matasan Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya halarci bikin cika shekaru 28 da rasuwar marigayi Shehu Musa Yar'adua
  • Atiku Abubakar ya yi muhimman jawabai a wajen taron inda ya jawo hankalin matasan Najeriya kan abin da ya kamata su sanya a gaba
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa har yanzu yana jin tasirin marigayi Shehu Musa Yar'adua a fagen siyasar Najeriya

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga matasan Najeriya da su tashi tsaye.

Atiku ya bukaci matasan da su kauce wa karaya kan yunkurin gina kasa ɗaya ta hanyar tattaunawa da jajircewa.

Atiku ya bukaci matasan Najeriya su tashi tsaye
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku ya yi wannan jawabin ne a wani rubutu da ya sanya a shafinsa na X a ranar Litinin, 8 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Barau ya jinjinawa Tinubu da sojojin Najeriya bayan dakile juyin mulki a Benin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya tuna da Shehu Musa Yar'adua

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kalaman ne yayin gabatar da muhimmin jawabi a bikin cika shekaru 28 da rasuwar Shehu Musa Yar’Adua.

Ya bayyana marigayin a matsayin “malami, abokin gwagwarmaya, kuma jagora” wanda tunaninsa har yanzu ke jagorantar tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya.

Atiku, wanda ke da kusanci na siyasa da Shehu Musa Yar’Adua, ya ce matasan Najeriya su yi koyi da adalci, daidaito da neman haɗin kai da Yar’Adua ya tsaya akai, maimakon rarrabuwar kai ta kabilanci ko ta yankuna.

“Shekaru 28 kenan tun da Shehu ya bar mu, amma har yanzu ina jin tasirinsa a cikin tattaunawar siyasar mu da a zukatan ‘yan Najeriya masu gaskiya da burin ganin ƙasar nan ta yi kyau."

- Atiku Abubakar

Wace shawara Atiku ya ba matasa?

Atiku ya roki matasa kada su fada cikin bakin ciki da takaici duk da kalubalen tattalin arziki da zamantakewa da ake fama da su, ciki har da tsadar rayuwa, rashin aiki, tsaro mai rauni, da ɓacin ran jama’a.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku Abubakar ya ziyarci Goodluck Jonathan'

“Ya kamata musamman matasanmu su fahimci cewa kasarmu ta sake samun kanta a wani yanayi. A yau muna fuskantar rashin aiki, rashin tsaro, ɓacin rai da rarrabuwar kai. Wasu sun gaji, da dama kuma sun rasa kwarin gwiwa.”
“Sakon Shehu gare ku shi ne: Kada ku daina yarda da kasarku. Kada ku daina yarda da junanku.”

- Atiku Abubakar

Atiku ya ba matasan Najeriya shawara
Atiku Abubakar a wajen bikin tunawa da marigayi Shehu Musa Yar'adua Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku ya bukaci matasa su zama masu tsara makomarsu, tare da taka rawar gani wajen karɓar jagoranci daga tsofaffin shugabanni domin su kammala aikin gina Najeriya mai adalci da karfafa haɗin kai.

“Don haka, ga kowane matashi ɗan Najeriya: ba ku da karamin karfi. Ba za ku tsaya gefe ku kalli yadda ake rubuta tarihin kasarku ba."
"Dole ne ku kasance marubuta, masu mafarki, masu aiki, kuma masu gina sabuwar Najeriya.”

- Atiku Abubakar

Dalilin da ya sa Atiku ya gana da Jonathan

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin Atiku Abubakar ya yi bayani kan dalilin da ya sa ubangidansa ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Paul Ibe ya bayyana cewa ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya kai wa Jonathan ba ta da alaka da siyasa.

Kara karanta wannan

Me ake kullawa: Atiku ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Ya bayyana cewa Atiku ya ziyarci Jonathan ne domin duba shi bayan dawowa daga aikin sa ido kan zaben shugaban kasar Guinea-Bissau.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng