Tawagar Amurka Ta Dauki Jiha 1 a Arewa, Ta Kawo Ziyara kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya
- Tawagar 'yan Majalisar Amurka ta kai ziyara jihar Benuwai a wani mataki na bincike kan zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi a Najeriya
- Gwamna Hyacinth Alia ya karbi tawagar a gidan gwamnatinsa da ke birnin Makurdi, kuma sun tattauna kafin su kai ziyara wata coci
- Dan majalisa Riley M. Moore ya ce sun gana da Bishof Wilfred Anagbe, Bishop Isaac Dugu da Mai Martaba Sarkin kabilar Tiv, James Ioruza
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue, Nigeria - Wata tawaga ta ’yan majalisar dokokin Amurka da sauran jakadu ta kawo ziyara Najeriya domin bincike kan zargin yiwa kiristoci kisan kare dangi a kasar.
Wannan tawaga ta Amurka ta wuce zuwa jihar Benuwai domin gano gaskiyar abin da ke faruwa kan zargin da ake yi na kokarin karar da kiristoci.

Source: Facebook
Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya tabbatar da ziyarar 'yan Majalisar Amurka a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar Amurka ta gana da Gwamna Alia
Gwamna Alia ya karɓe su a Birnin Makurdi ranar Asabar, inda suka yi wata ganawa ta sirri a cikin Gidan Gwamnati.
A wata sanarwa da gwamnan ya fitar bayan ganawa da tawagar 'yan Majalisar Amurka, Alia ya ce:
“Mun tattauna ne kan batutuwan tsaro da na jin kai da ke addabar jihar Benuwai da Arewa ta Tsakiya, da bukatar kawo zaman lafiya mai ɗorewa, adalci da tsaro ga mutanenmu.”
Daga baya tawagar ta kuma ziyarci Cocin Katolika da ke kusa da Gidan Gwamnati, inda suka sake wata ganawa ta sirri da Bishof Wilfred Anagbe na majami'ar Maki da wasu manyan limamai.
'Yan Majalisar Amurka da suka shigo Najeriya
Tawagar 'yan Majalisar dokokin Amurka ta ƙunshi, Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, Riley M. Moore da Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 19 za su tara Naira biliyan 19 duk wata, an jero abubuwan da za su yi a Arewa
Dan Majalisa Moore ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, inda ya ce:
"Girmamawa ne da muka samu damar ganawa da Bishof Wilfred Anagbe, Bishof Isaac Dugu da Mai Martaba James Ioruza, Sarkin al’ummar Tiv.”

Source: Twitter
Ribadu ya gana da tawagar Amurka
Lafin su tafi jihar Benuwai, tawagar ta gana da Mai Bada Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, a Abuja.
Wannan ganawar ta mayar da hankali ne kan batun yaƙi da ta’addanci, tsaron yankin Arewa da Sahel da karfafa dangantakar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka
Ribadu ya bayyana cewa tattaunawar ta ƙara gina aminci da haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu, tare da fatan hakan zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.
Bulama ya ba tawagar Amurka shawara
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen mai sharhi kan tsaro, kuma dan fafutukar kare hakkin dan adam, Barista Bulama Bukarti, ya yaba da ziyarar tawagar Amurka zuwa Najeriya.
Bukarti ya jaddada cewa tawagar ta gane wa idanunta yadda 'yan Najeriya ke rayuwa zai fi zama maifi dacewa a kan ta yi amfani da maganganun siyasa kawai.
Ya bada shawarar cewa ya kamata wannna tawaga ta yan Majalisar Amurka ta fadada ziyararta zuwa jihohin Arewa musamman wadanda ke fama da matsalar tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

