Akwai Matsala: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Ta'asa a Kano

Akwai Matsala: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Ta'asa a Kano

  • 'Yan bindiga na ci gaba da yin kutse daga Katsina zuwa wasu kauyukan jihar Kano, inda suke addabar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba
  • Tsagerun 'yan bindigan sun farmaki wani kauye da ke karamar hukumar Gwarzo inda suka yi awon gaba da wani dattijo
  • Mazauna yankin sun nuna damuwa kan hare-haren 'yan bindiga, inda suka yi kira ga gwamnatin Kano kan ta kawo musu daukin gaggawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a kauyen Kururawa da ke yankin Lakwaya, karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano.

'Yan bindigan sun yi garkuwa da wani dattijo manomi tare da jikkata ɗansa a harin da suka kai.

'Yan bindiga sun yi barna a Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta cewa wata majiya daga yankin, wadda ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da hakan ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun toshe kofofin tsiga ga 'yan bindiga a Sokoto, an hallaka tsageru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta bayyana cewa maharan waɗanda suka zo kan babura biyu kuma dauke da makamai sun shigo yankin ne daga jihar Katsina a daren ranar Lahadi.

Yadda 'yan bindiga suka kai hari

’Yan bindigan sun kutsa wani gida a Kururawa, inda suka yi garkuwa da wani tsohon manomi, Alhaji Yakubu Na Tsohuwa, bayan sun yi wa iyalansa fin karfi.

Hakazalika, 'yan bindigan sun harbi babban ɗansa mai suna Badamasi, a ƙafa yayin da yake kokarin hana su sace mahaifinsa.

An garzaya da Badamasi zuwa asibiti domin samun kulawar da ta dace, jaridar The Punch ta dauko labarin.

Majiyar ta ce yankin Lakwaya na da iyaka da Malumfashi da Musawa a Katsina, lamarin da ke sa yankin yawan fuskantar hare-haren daga 'yan bindigan da ke shigowa da ke jihohi makwabta.

“Kusan kilomita daya ne daga Kururawa zuwa Lakwaya. Sun shigo da daddare suka afka gidan inda suka tafi da Alhaji Yakubu. Ɗansa ya ji rauni yayin da yake kokarin kare shi bayan sun harbe shi, kuma an garzaya da shi zuwa asibiti."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari garuruwan Fulani 4 a Kaduna

- Wata majiya

Fargaba a cikin al’umma

Mutanen yankin sun bayyana wannan hari a matsayin na farko cikin dogon lokaci, amma ya jefa al’umma cikin tsoro da rashin tabbas.

Sun roƙi gwamnatin Kano ta gaggauta kafa cibiyar tsaro a yankin domin hana sake faruwar irin wannan hari.

'Yan bindiga sun kai hari a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Halin da ake ciki yanzu

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, rundunar ’yan sandan jihar Kano ba ta fitar da sanarwa ba game da lamarin.

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kano ba, CSP Abdullahi Kiyawa, domin bai ɗauki kiran da aka yi masa ba.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindiga a jihar Sokoto.

Dakarun sojojin sun hallaka 'yan bindiga da dama bayan sun yi yunkurin sace wasu 'yan kasuwa da ke kan hanyar zuwa neman na abinci a karamar hukumar Sabon Birni.

Kara karanta wannan

'Yan bindigan da suka sace amarya da kawayenta sun turo sako a jihar Sakkwato

Hakazalika, sojojin sun samu nasarar kwato babura da makamai daga hannun 'yan bindigan bayan sun fatattake su zuwa cikin daji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng