Tinubu Ya Yi Maraba da Ceto Daliban Neja, Ya Ba Jami'an Tsaro Sabon Umarni
- Wasu daga cikin daliban da 'yan bindiga suka sace a jihar Neja sun shaki iskar 'yanci bayan sun kwashe kwanaki a hannun tsageru
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa jami'an tsaro bisa kokarin da suka yi wajen kubutar da daliban wadanda aka sace cikin dare a makaranta
- Mai girma Bola Tinubu ya kuma taya gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, murnar ganin yaran sun dawo cikin koshin lafiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi martani bagan ceto dalibai 100 daga cikin wadanda 'yan bindiga suka sace a Neja..
Shugaba Tinubu ya yaba wa hukumomin tsaro bisa kokarin da suka yi wajen kubutar da dalibai 100 na makarantar Katolika da aka kai wa hari a jihar Neja.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X, a ranar Litinin, 8 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni
Yayin da yake nuna farin cikinsa kan dawowar daliban, Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su hanzarta ceto sauran dalibai 115 da malamansu da har yanzu suke tsare a hannun ’yan bindiga.
A cewar Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa iyayen daliban cewa gwamnatin tarayya da ta jihar Neja na aiki tare domin ganin an mayar da dukkan yaran gidajensu lafiya.
“An ba ni rahoton dawowar dalibai 100 na makarantar Katolika da ke jihar Neja. Ina taya Gwamna Umar Bago farin ciki, kuma ina yabawa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen ganin an dawo da yaran tun bayan harin da aka kai ranar 21 ga Nuwamba."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasar ya ce umarninsa ga jami’an tsaro bai sauya ba kan ceto daliban da aka sace.
“Dole ne dukkan daliban da sauran ’yan Najeriya da aka yi garkuwa da su a fadin kasa a ceto su, a dawo da su gida lafiya. Sai mun tabbatar da an samo su gaba ɗaya."
- Shugaba Bola Tinubu
Gwamnatin Tinubu za ta kula da tsaro
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tare da jihar Neja da sauran jihohi domin tsare makarantu a kasar nan da kuma tabbatar da ingantaccen tsaro ga ɗalibai.

Source: Facebook
“Daga yanzu, dole ne hukumomin tsaro tare da hadin guiwar gwamnonin jihohi su dakile duk wani yunkurin sace dalibai nan gaba."
"Ba za mu yarda yaranmu su ci gaba da zama kamar ganima a gaban ’yan ta’adda marasa tausayin da ke neman dakile iliminsu da jefa su da iyayensu cikin tashin hankali ba.”
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya gana da Gwamna Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.
Mai girma Bola Tinubu ya gana da Gwamna Fubara ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Ganawar ta su dai na zuwa ne bayan mafi yawa daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Rivers sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


