Gwamna Fubara Ya Sa Labule da Tinubu bayan Sauya Shekar 'Yan Majalisa zuwa APC
- Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya garzaya zuwa fadar shugaban kasa domin ganawa da Mai girma Bola Ahmed Tinubu
- Siminalayi Fubara ya gana da shugaban kasar ne yayin da ake rade-radi kan cewa akwai yiwuwar ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
- Ganawar ta su dai na zuwa ne bayan wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Rivers sun tsallaka daga PDP zuwa jam'iyyar APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Siminalayi Fubara ya gana da Mai girma Bola Tinubu ne a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Source: Facebook
Gwamna Fubara ya gana da Tinubu
Jaridar The Punch ta ce wakilinta ya hango gwamnan yana tafiya cikin haraba zuwa ofishin shugaban kasa da misalin karfe 5:01 na yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan yana sanye da riga mai dogon hannu launin shuɗi mai duhu, wando baki, da hula mai launin baki.
‘Yan mintoci kafin hakan, an shigar da gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, domin wata ganawa daban, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
Har yanzu ba a bayyana cikakken bayanin abin da aka tattauna ba a tsakanin shugaban kasar da Gwamna Siminalayi Fubara.
Ana jita-jita kan sauya shekar Gwamna Fubara
Ziyarar ta zo ne a dai-dai lokacin da ake ta rade-radin cewa Gwamna Fubara na iya ficewa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC, sakamakon sabon rikicin siyasa a jihar.
A ranar Jumma’a, 5 ga watan Disamba, ‘yan majalisa 17 da ke goyon bayan Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisa, Martin Amaewhule, sun sanar da ficewarsu daga PDP zuwa APC.
Lamarin da ya sauya rinjayen majalisar nan take, inda jam'iyyar APC ta karbe rinjaye daga hannun PDP.
'Yan majalisa guda uku da ake ganin suna goyon bayan Gwamna Fubara ba su koma zaman majalisa ba tun bayan dage dokar ta-baci a jihar a ranar 18 ga Satumban 2025.
Rashin komawar ta su ya kara haifar da tambayoyi kan makomar siyasar gwamnan.

Source: Twitter
A baya, an dawo da Gwamna Fubara kan kujerarsa bayan kawo karshen dokar ta-bacin da Shugaba Tinubu ya kakaba a ranar, 18 ga watan Maris 2025.
Nwifuru kuwa, gwamna ne na APC kuma tsohon shugaban majalisar dokokin Ebonyi, wanda shima ya yi ta kai ziyara fadar shugaban kasa a watannin baya kan batun ayyukan more rayuwa da tsaro a yankin Kudu maso Gabas.
Gwamnatin Tinubu ta ba da lamuni
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ba da lamuni ga malamai da ma'aikatan jami'o'i.
Gwamnatin ta tabbatar da raba sama da naira biliyan 3.7 a matsayin lamuni ga malamai da ma’aikatan jami’o’i, kwalejojin fasaha da kuma kwalejojin ilimi a karkashin shirin TISSF.
An dai An kaddamar da shirin a watan Agustan shekarar 2025, tare da ba da damar karbar lamunin har zuwa N10m ba tare da riba ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

