Gwamnoni 19 Za Su Tara Naira Biliyan 19 duk Wata, An Jero Abubuwan da Za Su Yi a Arewa
- Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun yunkuro da nufin kawo kashen matsalar tsaron da ta addabi al'ummar yankin gaba daya
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce sun amince kowane gwamna zai rika ba da Naira biliyan 1 a kowane wata
- Ya ce za a yi amfani da kudin wajen samar da kayan aiki na zamani, daukar matasa 'yan sa-kai da sauran matakan yaki da matsalar tsaro a Arewa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa, Nigeria - Kungiyar gwamnonin jihohin Arewa 19 ta tashi tsaye da zummar kawo karshen hare-haren 'yan bindiga, Boko Haram da sauran matsalolin tsaro a yankin.
Gwamnonin sun kafa sabon asusun tsaro na hadin gwiwa domin tara kudin da za a yi amfani da su a harkokin samar da tsaro a Arewacin Najeriya.

Source: Facebook
Gwamnonin Arewa sun kafa asusun tsaro
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kowane gwamna zai rika bada Naira biliyan 1 a wata, jimulla za a rika tara Naira biliyan 19 a kowane wata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya bayyana haka a zaman majalisar zartarwar jihar da aka yi a Lafia.
Abubuwan da za su yi da kudin a Arewa
Gwamna Sule ya ce an cimma matsayar ne domin siyan kayan fasaha na zamani don taimakawa jami’an tsaro, daukar matasa 'yan sa-kai aikin tsaro, Inganta hadin kai a yaki da ta’addanci, fashi, da satar shanu.
Ya ce:
“Mun yanke shawarar kowane gwamna zai rika ba da N1bn kowane wata saboda dole mu dauki yaki da matsalar tsaro da hannu biyu-biyu. Idan ba mu dauki mataki ba, matsalar za ta iya fin karfinmu."
Jimillar kudin da jihohin Arewa za su rika tarawa a kowane wata shi ne Naira biliyan 19 kuma za su kwashe shekara guda suna hada wannan kudi a asusun hadin gwiwa.
Za a gina sakatariyar kungiyar NGF
Sule ya bayyana cewa Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayar da fili a wuri mai muhimmanci domin gina Sabon Ofishin Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF).

Kara karanta wannan
Gwamna Inuwa ya yi karatun ta natsu, ya zakulo abin da ya haddasa rashin tsaro a Arewa
Gwamnan ya ce kowace jiha za ta bayar da N100m a wannan wata na Disamba domin share filin, da gina tubalin farko na ginin sakatariyar.
Ya ce duk tarurrukan kungiyar gwamnonin Arewa ana yinsu ne a gidan gwamnatin Kaduna, amma yanzu lokaci ya yi da ya kamata kungiyar ta mallaki ofis.

Source: Twitter
Kungiyar ta kuma nada Cif Ezekiel Gomos, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Filato a matsayin Darakta Janar na kungiyar gwamnonin Arewa.
Gwamna Sule ya ce Gomos, shi ne zai kula da kudaden tsaro da dukkan shirye-shiryen hadin gwiwa na gwamnonin Arewa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Gwamna Sule zai kafa 'yan sandan jiha
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Abdullahi Sule ta bayyana cikakken shirinta na kafa ’yan sandan jiha a Nasarawa.
Kwamishinan tsaro da harkoki na musamman na jihar Nasarawa, CP Usman Baba (mai ritaya), ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Lafiya.
Kwamishinan ya jaddada cewa Gwamna Sule ya kuduri aniyar tabbatar da cewa jihar ta kasance mai aminci ga masu zuba jari da kuma zaman lafiya ga ’yan ƙasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
