Bayan Kwanaki 4, An Samu Labarin Rasuwar Tsohon 'Dan Majalisar Tarayya a Najeriya

Bayan Kwanaki 4, An Samu Labarin Rasuwar Tsohon 'Dan Majalisar Tarayya a Najeriya

  • An samu labarin rasuwar tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Sakkwato kuma dagacin garin Wajake, Muhammad Mai Lato
  • Basaraken ya rasu ne a ranar Alhamis da ta gabata kuma tuni aka masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada
  • Gwamna Ahmed Aliyu da manyan kusoshin APC, malamai, sarakuna da dumbin jama'a sun halarci addu'ar fidda'u yau Litinin, 8 ga watan Disamba, 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Jihar Sokoto ta shiga cikin jimami bayan rasuwar Muhammad Mai Lato, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya a zamanin Jamhuriyya ta biyu.

Muhammad Mai Lato, ya kasance shi ne dagacin garin Wajake da ke Karamar Hukumar Wamakko a jihar Sakkwato kafin Allah ya karbi rayuwarsa.

Muhammad Mai Lato.
Marigayi Muhammad Bello Mai Lato da mutanen da suka halarci addu'ar uku Hoto: Ahmad Bello Madunga
Source: Facebook

Tsohon dan Majalisa ya rasu

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Mai Lato ya rasu ne a ranar Alhamis da ta gabata, 4 ga watan Disamba, 2025 a Abuja bayan doguwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi babban rashi, tsohon Sanata a Arewa ya riga mu gidan gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni aka yi wa tsohon dan Majalisar tarayya jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada a mahaifarsa da ke jihar Sakkwato.

A ranar Litinin, 8 ga Disamba, 2025 aka gudanar da adu’ar fidda’u ta uku a Gumbi, Wamakko, karkashin jagorancin Sarkin Malaman Sakkwato, Sheikh Yahaya na Malam Boyi, tare da wasu fitattun malamai.

Gwamna Ahmed ya halarci addu'ar uku

Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya halarci taron addu’a tare da manyan ’yan siyasa da jami’an gwamnati, ciki har da tsohon gwamna kuma jagoran APC, Sanata Aliyu Wamakko,

Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, Kakakin Majalisar Jihar Sakkwato, Rt. Hon. Tukur Bala Bodinga, da Mataimakinsa, Kabir Ibrahim Kware sun halarci taron addu'an.

Haka zalika, dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Gudu da Tangaza, Hon. Sani Yakubu, shi ma ya samu halartar taron nema wa mamacin rahama.

Sauran da suka halarta sun hada da Sakataren Gwamnatin Sakkwato, Muhammad Bello Sifawa, jiga-jigan APC, kwamishinoni, shugabannin kananan hukumomi, masu ba da shawara, malamai, ’yan siyasa da dimbin masoyan marigayin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura sako na musamman ga Majalisa bayan tabbatar da nadin ministan tsaro

Gwamna Ahmad Aliyu.
Gwamna Ahmed Aliyu tare da Sanata Wamakko a wurin taron addu'ar uku Hoto: Ahmad Bello Madunga
Source: Facebook

An yi masa addu'ar neman rahama

A zamaninsa, Muhammad Mai Lato ya kasance shugaba mai mutunci da jajircewa wajen hidimtawa al’umma tun daga majalisar tarayya har zuwa lokacin da ya ama dagacin Wajake.

Ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya 22, sannan manyan mutane ciki har da Gwamna Ahmed Aliyu sun yi addu'ar Allah ya jikansa da rahma, ya ba iyalansa hakuri, cewar Daily Post.

Tsohon sanata, Isa Obaro ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Isa Abonyi Obaro, wanda ya wakilci mazabar Okehi/Okene a tsohuwar jihar Kwara, ya rasu bayan ya sha fama da jinya.

Sanata Obaro ya yi wa jam’iyyar NPN hidima a matsayin dan majalisa mai wakiltar tsohuwar Kwara ta Kudu da yanzu ita ce Kogi ta Tsakiya.

Haka kuma, ya rike manyan mukamai a majalisar zartarwa ta jihar Kwara daga 1968 zuwa 1975, inda ya nuna jajircewa da kishin kasa wajen gudanar da ayyukan gwamnati da raya al’umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262