To Fa: Gwamna Fintiri Ya Kakaba Dokar Ta Baci a Adamawa, an Ji Dalili
- An samu barkewar rikicin kabilanci a jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas da yammacin ranar Lahadi
- Gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi gaggawar daukar mataki ta hanyar sanya dokar ta baci ta tsawon awa 24
- Hakazalika, Gwamna Fintiri ya umurci jami'an tsaro da su gaggauta zuwa yankin da lamarin ya auku domin dawo da doka da oda
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri, ya ayyana dokar ta-ɓaci ta awanni 24.
Gwamna Fintiri ya sanya dokar ta bacin ne a karamar Hukumar Lamurde, bayan sake barkewar rikicin kabilanci a yankin.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na mataimakin gwamna, Hussaini Hammangabdo, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, 8 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fintiri ya ba jami'an tsaro umarni
Gwamna Fintiri ya umarci jami’an tsaro da su hanzarta shiga yankunan da abin ya shafa domin dawo da zaman lafiya da doka da oda, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da hakan.
Sanarwar ta ce Gwamna Fintiri ya umurci jami’an tsaro da su garzaya yankunan da ke fuskantar sabon rikicin domin tabbatar da cewa an dakile tashin hankalin cikin gaggawa.
Meyasa aka sanya dokar ta baci a Adamawa?
“Gwamnatin jihar Adamawa ta kakaba dokar ta ɓaci ta awa 24 a karamar hukumar Lamurde nan take, bayan sake barkewar rikicin da ya faru da yammacin ranar Lahadi."
"Bisa sa hannun Hussaini Hammangabdo, sakataren yaɗa labarai na mataimakin gwamna, an umurci jami’an tsaro da su shiga yankin domin dawo da zaman lafiya ba tare da ɓata lokaci ba.”
- Hussaini Hammangabdo

Source: Twitter
Gwamnati ta roki mazauna Lamurde da su kwantar da hankalinsu tare da ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai, domin a tabbatar rikicin bai sake karuwa ko ya bazu zuwa wasu yankuna ba.

Kara karanta wannan
Gwamna Inuwa ya yi karatun ta natsu, ya zakulo abin da ya haddasa rashin tsaro a Arewa
Karanta wasu labaran kan Adamawa
- Gwamna Fintiri ya bayyana abu na 2 da ya fi kauna a rayuwarsa bayan addinin musulunci
- Gwamna Fintiri ya yi afuwa ga masu laifi don murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yanci
- Sabuwar cuta mai cin naman jiki ta bulla a Adamawa, gwamnati ta fara bincike
- Majalisa ta kara wa gwamna karfi, ta sauya dokar nadawa da sauke Sarki daga mulki
Gwamna Fintiri zai tura dalibai kasar waje
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Adamawa karkashin jagorancin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ta amince da daukar nauyin dalibai 100 ‘yan asalin jihar su yi karatun digirin PhD a kasar Turkiyya.
Kwamishinan yada labarai, James Iliya ya bayyana cewa shirin tallafin karatun na cikin kokarin gwamna Fintiri na bunkasa ilimi da gina hazikan matasa da za su kara wa jihar ma’aikata a fannoni masu muhimmanci.
Hakazalika, kwamishinan ya bayyana cewa shirin zai ba daliban damar yin karatu a manyan jami’o’in kasar Turkiyya, domin samun kwarewar zamani da za su dawo su yi amfani da ita a gida.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
