Yajin Aikin PENGASSAN Ya Jawowa Injiniyoyin Dangote, An Hana Su Albashi
- Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta PENGASSAN ta shiga damuwa bayan yajin aikin da ta yi a kwanakin baya ya bar baya da kura
- Rahotani sun tabbatar da cewa Dangote ya dakatar da biyan albashin injiniyoyin da aka kora bayan takaddama da ta shiga tsakani da PENGASSAN
- Kungiyar da saboda ita ne aka samu wannan matsala ta bayyana irin matakan da ta ke dauka domin shawo kan matsalar a cikin ruwan sanyi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Rahotanni sun nuna cewa matatar man fetur ta Dangote ta dakatar da biyan albashin injiniyoyin da ta sallama a watan Satumba.
Matatar ta sallami wadannan injiniyoyi ne sakamakon rikicin da ya barke da kungiyar ma'aikatan mai ta PENGASSAN.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan mataki ya biyo bayan yadda ma’aikatan suka ƙi karɓar sabon aikin da aka tura su zuwa wasu jihohi kamar Zamfara, Borno, Binuwai, Sakkwato da sauran su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara sauya wurin aikin injinoyoyin Dangote
Wasu daga cikin ma’aikatan da suka nemi a sakaya sunansu sun ce an tura wasu daga cikinsu zuwa wuraren hako kwal a Binuwai.
Wasu kuma an aika su wurin gina titunan kankare a Borno da Ebonyi, da kuma shuke-shuken shinkafa a Kebbi, Neja, Sakkwato da Zamfara.
Kaɗan ne suka amince, yayin da mafi rinjaye suka dogara da jami’an PENGASSAN cewa a warware lamarin ta tattaunawa.

Source: Getty Images
Rahoto ya nuna cewa kamfanin Dangote ya soma rage musu albashi tun a watan Oktoba kafin daga bisani ya dakatar da biyan kudin watan Nuwamba gaba ɗaya.
Wani babban jami’in kamfanin ya tabbatar da cewa ba za a ci gaba da biyan ma’aikatan da suka ƙi karɓar sabon guraben aikin ba.
Rikicin PENGASSAN da Dangote ya kara tsananta
A watan Satumba ne PENGASSAN ta rufe wasu muhimman cibiyoyin man fetur kan zargin sallamar kusan ma’aikata 800 saboda shiga ƙungiyar kwadago.
Dangote ya musanta zargin, yana cewa gyaran tsarin aiki ne kawai. Rufe wuraren ya janyo asarar man fetur da wutar lantarki a faɗin ƙasa.
A watan Oktoba, an gayyaci injiniyoyin da aka sallama su karɓi takardar sabon horo a ofishin Ikeja, inda aka tabbatar masu da sauyin wurin aiki.
Amma ma’aikatan sun ce ba a ba su adireshin ofishi da aka aika su a Binuwai ba, kuma yankunan da aka tura su suna da matsalar tsaro.
Sun ce:
“Idan ka karɓi takardar, kai da kanka ka sallami kanka, domin babu ofishin da za ka je.”
Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, ya ce suna ci gaba da tattaunawa da Dangote domin a warware matsalar a cikin ruwan sanyi.
Ya ce:
“Muna fatan magance rikicin a teburin sulhu, ba tare da sake komawa yajin aiki ba.”
Matatar Dangote ta rage farashin mai
A baya, kun samu labarin cewa Matatar mai ta Dangote ta musanta zargin da ake yadawa cewa ta rage farashin mai ne saboda gwamnati ta soke harajin shigo da man fetur.
A cewar kamfanin, wannan magana ba ta da tushe, kuma ba ta da alaƙa da gaskiyar abin da ke faruwa a kasuwar mai da ya jawo saukar farashin litar man fetur a kwanakin baya.
Dangote ya bayyana cewa dalilin saukar farashi shi ne sauyin da ya faru a kasuwa, wanda ya ba kamfanin damar yin ragi na 5.6% a farashin mai, amma ba batun haraji ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


