Obasanjo Ya Bada Kafa kan Shekarun da Yake da Su a Duniya
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi tsokaci kan shekarun da yake da su a duniya
- Obasanjo ya bayyana cewa bai san shekarun da yake da su a duniya ba amma ya ba da satar amsar yadda za a iya ganowa
- Tsohon shugaban kasar ya kuma nuna muhimmancin adana kayan tarihi domin al'ummar da za su zo nan gaba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan shekarun da yake da su a duniya.
Obasanjo ya sake jaddada cewa ba ya da tabbaci kan ainihin shekarun da yake da su na haihuwa duk da tsawon rai da ya yi.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Disamban 2025 yayin tattaunawa da Toyin Falola.
Tattaunawar ta samu jagorancin Farfesa Toyin Falola, fitaccen masanin tarihin Najeriya, tare da Dr. Mathew Kukah, da kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Farfesa Kingsley Moghalu.
Yadda Obasanjo yake gane shekarunsa
Obasanjo ya ce yana tantance shekarunsa ne ta hanyar kallon shekarun tsofaffin abokansa na firamare da suka rage a duniya, inda ya ce mutum shida daga cikinsu suna raye, kuma babu wanda shekarunsa suka gaza 90.
“Ban san ainihin shekaruna ba, amma ina iya danganta su da wadanda muka yi makaranta tare. Misali, Olubara (Oba Jacob Olufemi Omolade) yana raye."
"Ina ganin akwai mutum shida da muka yi makarantar sakandare tare, dukkansu suna da fiye da shekara 90. Don haka ku yi hasashe da kanku.”
- Olusegun Obasanjo
Meyasa Obasanjo ya kafa dakin karatu?
Obasanjo ya kuma bayyana cewa ya kafa dakin karatu na shugaban kasa ne domin a adana tarihi, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Mun adana fiye da kayan tarihi miliyan uku a yanar gizo, kuma muna da kusan wannan adadi da za mu adana. Manufar ita ce wadannan bayanai su kasance a yanar gizo don jama’a su iya amfani da su.”
- Olusegun Obasanjo

Source: Twitter
Ya kara da cewa dakin karatun yana dauke da takardun karatunsa na firamare, Takardun sakandare, wasikarsa ga Abacha lokacin da dansa ya rasu, wasikarsa ga matarsa lokacin yana kurkuku da rubuce-rubucensa da ya yi a gidan yari.
Ya ce rashin adana tarihi da rubutattun bayanai babbar matsala ce a Najeriya.
“Dalilin kafa dakin karatu na shugaban kasa shi ne don magance matsalar rashin adana tarihi. A al’ummarmu ba mu da kyakkyawan tsarin adana bayanai, kuma ba mu da cibiyoyi masu yin hakan."
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya soki tattaunawa da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi fatali da maganganun da ake yi na gwamnati ta tattauna da 'yan bindiga.
Obasanjo ya bukaci gwamnatin tarayya ta daina neman uzuri kan matsalar rashin tsaro da kuma tattaunawa da ’yan ta’adda.
Tsohon shugaban kasar ya nuna takaici kan yadda tsaro ke tabarbarewa, yana mai cewa ’yan Najeriya suna da hakkin neman taimakon kasashen duniya idan gwamnati ta kasa kare su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

